Tinubu Ya Bayyana Yadda Zai Kashe Bashin Dala Biliyan 3.5 Daga Bankin Duniya

Tinubu Ya Bayyana Yadda Zai Kashe Bashin Dala Biliyan 3.5 Daga Bankin Duniya

  • Ministan kudade a Najeriya, Wale Edun ya bayyana tsarin da za a bi wurin kashe bashin dala biliyan 3.5 daga Bankin Duniya
  • Ya ce kudaden za a yi amfani da su ta hanyoyi da dama da su ka hada da inganta wutar lantarki da makamashi da sauransu
  • Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC ta kuma amince da bude asusun agajin mutane da kuma dakile talauci a tsakanin al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja – Yayin taron majalisar zartarwa ta FEC, majalisar ta amince da yin amfani da kudaden da za a karbo bashi dala biliyan 3.5 daga Bankin Duniya.

A jiya Litinin 23 ga watan Oktoba majalisar ta amince da yin amfani da kudaden ta hanyoyi biyar ma su muhimmanci a kasar, Legit ta tattaro.

Tinubu ya yi bayanin yadda zai kashe bashin dala biliyan 3.5 daga Bankin Duniya
Gwamnatin Tarayya ta yi bayanin yaddda za ta kashe kudaden da za ta karbo bashi. Hoto: FG.
Asali: UGC

Ta yaya Tinubu zai kashe kudaden daga Bankin Duniya?

Kara karanta wannan

Jerin Manyan 'Yan Takara 5 da Jam'iyyun da Za Su Fafata a Zaben Jihar Kogi a Wata Mai Kamawa

Hanyoyin da za a kashe kudaden sun hada da inganta rayuwar mata da harkar wutar lantarki da samar da makamashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da kula da ilimin yara mata da inganta rayuwarsu da harkokin wayar da kan jama’a.

Ministan Kudade a kasar, Wale Edun ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta karbi bashin wanda ba shi da kudin ruwa ko kadan inda kuma zai dauki tsawon shekaru 10 kafin fara biya.

Yaushe za a fara biyan bashin da Tinubu ya karba?

Har ila yau, tsawon lokacin da Najeriya za ta kwashe ta na biyan bashin Bankin Duniya zai kai shekaru fiye da 40, cewar Channels TV.

Edun ya bayyana cewa za a fara biyan basukan a shekarar 2033 inda dala miliyon 700 zai taimakawa yara mata da ke sakandare samun koyan sana’o’i.

Kara karanta wannan

Za a Kawo Karshen Tashin Dala, Ana Sa Ran Shigowar $10bn Nan da ‘Yan Makonni

Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin ta yi alkawarin tsame miliyoyin mutane daga gankin talauci a Najeriya musamman matasa.

‘Za mu fara ba da lamunin dalibai a watan Janairu, Tinubu

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa zai fara shirin ba da lamunin karatun dalibai a watan Janairun 2024.

ShugabaN ya bayyana cewa wannan shiri zai dakile yawan yajin aiki da ake yi a manyan makarantun kasar baki daya.

Dalibai na dakon fara wannan shirin tun bayan rattaba hannu da Shugaba Tinubu ya yi a farkon hawanshi karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.