Yadda Shugaba Tinubu Ya Cusa Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya a Aljihunsa

Yadda Shugaba Tinubu Ya Cusa Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya a Aljihunsa

  • Bola Ahmed Tinubu ya samu yadda yake so a majalisar tarayya bayan ya dare kan kujerar shugaban kasa a karshen Mayun 2023
  • Kafin ya hau mulki, Shugaban Najeriyan ya gujewa kuskuren da magabacinsa Muhammadu Buhari ya yi tun lokacin zaben 2015
  • Mai girma Tinubu ba zai rasa ta-cewa a majalisa ba, mutanensa ke rike da shugabanci, mukamai da kuma manyan kwamitoci

Abuja - Bai cika watanni biyar da hawa kan karagar mulki ba, amma alamu sun nuna Bola Ahmed Tinubu ya samu yadda yake so a majalisa.

Aikin ‘yan majalisa shi ne yin dokoki da kuma sa ido a ayyukan zartarwa, Sun ta ce mutanen Bola Ahmed Tinubu ke kankame da majalisun.

Baya ga shugabanni hudu da ake da su a majalisar dattawa da na wakilan tarayya, na-kusa da shugaban kasa sun rike manyan kwamitoci.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki Ya Kare: Tinubu Ya Bayyana Ranar Fara Shirin Lamunin Dalibai, Ya Fadi Amfanin Shirin

Tinubu Majalisar Tarayya
Godswill Akpabio da Femi Gbajabiamila a Majalisa Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Tun farko Godswill Akpabio da Tajudeen Abass su ka samu kujerun majalisar, wadanda su ka yaki ‘yan takaran ba su yi nisa a zaben bana ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa: Opeyemi ya sha gaban Sanata Ndume

An yi tunanin Mohammed Ali Ndume zai koma kujerar shugaban masu rinjaye, kwatsam sai aka ji tsohon hadimin Tinubu ya samu mukamin.

A majalisar wakilai, Julius Ihonvbere ya samu kujerar, jaridar ta ce APC ba ta goyi bayan haka ba, amma fadar shugaban kasa ta hakikance.

Mutanen Tinubu sun tashi da kwamitocin Majalisa

Wata majiya ta ce magoya bayan shugaban Najeriyan sun samu rikon kwamitoci masu tsoka ne saboda gudun a kawowa gwamnati cikas.

Na-kusa da Tinubu su ke jagorantar kwamitocin kasafin kudi, tattalin arziki, harkar banki, kula da bashi da kuma na harkokin kasashen waje.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fara Sabon Yunkuri Domin Hana Amurka Fallasa Ragowar Sirrinsa a Duniya

A cewar wani ‘dan majalisa, gwamnatin Tinubu za ta aiko da kudirorin yi wa kudin tsarin mulki garambawul da kuma bukatar cin bashin kudi.

An manya da Sanatocin Ibo a Majalisa?

Bayan nada David Umahi a matsayin Minista, maimakon wani daga Kudu maso gabas ya hau kujerarsa, sai aka dauko Oyelola Yisa Ashiru.

Duk da APC ta na da Sanatoci rurutu daga kudu maso gabas, duk an yi watsi da su, aka zabo mataimakin Bamidele daga Arewa maso tsakiya.

An taso Tinubu a gaba a kasar waje

A baya aka samu labari Aaron Greenspan da David Hundeyin sun nemi bayanin wata shari’a da aka yi da Bola Tinubu a kotun Illinois a Amurka.

A shekarar 1993, aka zargi Shugaban Najeriya da harkar miyagun kwayoyi. Yanzu Hukumar FBI za ta fitar da rahoto da zai nuna abin da ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel