Dangin Wata Bazawara Sun Yi Wa Tsohon Mijinta Duka Har Lahira a Jihar Neja
- Wani mutum ya rasa ransa sakamakon dukan da dangin tsohuwar matarsa suka yi masa a garin Minna, jihar Neja
- Mallam Umar Tasiu ya je ganin yaransa da ke hannun matarsa da suka rabu lokacin da surukan nasa suka dungi dukansa har sai da ya daina shurawa
- Sai dai kuma, rundunar yan sandan jihar ta ce yan daba ne suka farmaki marigayin
Jihar Niger - Rahotanni sun kawo cewa wani mutum mai suna Mallam Umar Tasiu ya rasa ransa, sakamakon dukan da dangin tsohuwar matarsa suka yi masa a garin Minna, babban birnin jihar Neja.
An tattaro cewa mutumin ya je ganin yaransa biyu a gidan iyayen tsohuwar matar tasa lokacin da suka far masa da duka har sai da ya daina shurawa.
Lamarin ya afku ne a daren tanar Asabar inda ya rasu bayan an kwashe shi zuwa asibitin kwararru na IBB.
Magidanci ya rasa ransa sakamakon dukan da dangin tsohuwar matarsa suka yi masa
Wani makwabcin su da ya nemi a sakaya sunansa ya fada ma jaridar Daily Trust cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ya je ganin yaransa guda biyu wadanda ke zama da tsohuwar matarsa a gidan mahaifinta. Sun rabu amma yaran na zama ne da mahaifiyarsu. Ya je ganinsu sannan tsoffin surukansa da basa son ganinsa a gidansu suka daure shi sannan suka dungi zane shi har sai da ya mutu a gidansu. An dawo da gawarsa gidansu a daren ranar Asabar kuma mun binne shi a ranar Lahadi da misalin karfe 10:00 na safe."
Rundunar yan sanda ta yi martani
Sai dai kuma, rundunar yan sandan jihar ta fada ma City & Crime cewa mutumin ya mutu ne bayan an kwashe shi zuwa asibitin kwararru na IBB da ke garin Minna sakamakon raunin da yan daba suka ji masa.
Kakakin yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya ce:
"A ranar 22/10/2023 da misalin karfe 0800hrs an kai wa sashin rundunar GRA rahoton wani kisa da ake zargin an yi a gida a ranar 21/10/2023 da misalin 2300hrs, yan daba sun farmaki wani Umar Tasiu na Angwan Daji a Minna sannan suka ji masa raunuka daban-daban. An kwashe shi zuwa asibitin IBB, Minna, inda ya rasu. Ana kan bincike cikin lamarin da kama wadanda ake zargi."
Shugaba da mataimakin shugaban makaranta sun shiga hannu kan dukan dalibi har lahira a Zaria
A wani labarin kuma, mun ji cewa yan sanda sunm cika hannu da wani shugaba da mataimakin shugaban wata makaranta a garin Zaria.
Hakan ya biyo bayan zane wani dalibi da ake zargin sun yi har lahira saboda ya yi fashin zuwa makaranta.
Asali: Legit.ng