Matar Aure Ta Haifi Tagwaye Bayan Shekaru 14 Da Aure, Yan Kasuwa Sun Yi Wa Mijin Wanka Da Hoda

Matar Aure Ta Haifi Tagwaye Bayan Shekaru 14 Da Aure, Yan Kasuwa Sun Yi Wa Mijin Wanka Da Hoda

  • Wasu mata sun kaure da murna a kasuwa yayin da Allah ya azurta wani mutum da matarsa da haihuwar tagwaye bayan shekaru 14 da aure
  • Mata yan kasuwar sun yi wa mutumin wanka da hoda domin taya shi murnar wannan babban ni'ima da Allah ya yi masa a rayuwa
  • Yan TikTok da dama da suka kalli bidiyon sun ce abun ya taba zukatansu yayin da suka roki Allah ya yi irin haka ga masu neman haihuwa

Allah ya azurta wasu iyali da suka shafe tsawon shekaru 14 suna jiran tsammani da haihuwar tagwaye.

Mata yan kasuwa da dama sun cika da murna lokacin da suka ga angon karnin. Sun zazzaga masa hoda tun daga kar don taya shi murna.

An yi wa mijin matar wanka da hoda
Matar Aure Ta Haifi Tagwaye Bayan Shekaru 14 Da Aure, Yan Kasuwa Sun Yi Wa Mijin Wanka Da Hoda Hoto:@viviluv9
Asali: TikTok

Mutane sun yi murnar haihuwar tagwaye

Yan kasuwa da suka san matar sun kaure da ihun murna. Ma'aikaciyar mai jegon ta fasa ihu:

Kara karanta wannan

“Ba a Jin Kanmu”: Kawaye Biyu Na Soyayya Da Saurayi Daya, Sun Yi Sharholiya Da Shi a Bidiyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Uwar dakina ta haihu."

Farin cikin da ya karade kasuwar ya kasa boyuwa a cikin bidiyon TikTok. Mutane da dama sun kasance dauke da hoda a fuskokinsu wanda ke nuna suna taya ma'auratan murna. @viviluv9 ce ta yada bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Bishop_Zoid ta ce:

"Kada wanda ya yi wasa da yaran nan saboda rundunar yan kasuwa ne a bayansu faaaa. Ni dai na fadi nawa."

mercy 2 ta ce:

"Na rokawa kawuna wannan. Shekaru 25."

I’m blessed ta ce:

"Wa ke kukan murna tare da ni."

Sandra Justin 29 ta ce:

"Ina rokon Allah ya albarkaci antina da haihuwar da."

King Howells ya ce:

"Zai zamana jinsina da dama sun haifi kamar yara 3 da wata matar a cikin wannan shekaru 14 din...Na taya su murna."

Kara karanta wannan

“Ba Ki Da Hankali Ne?” Wani Mutum Ya Kurma Ihu Bayan Ya Kama Mai Aiki Tana Wanke Masa Kayan Wuta Da Sabulu

Laura ta ce:

"Ba za ka fahimci irin wannan farin cikin ba idan ba wai ka zauna da ma'auratan da ke jiran tsammani bane. Na taya ku murna. Duk ma'auratan da ke jiran tsammani za su yi murna haka."

Yar Najeriya ta yi wuff da angonta dan Koriya

A wani labari na daban, mun ji cewa wani mutumin kasar Koriya da ya auri Bayarabiya ya kayatar da mutane da dama a ranar aurensa yayin da ya yi shigowar kasaita tare da yan uwa da abokansa.

Gaba daya abokan angon sun sanya babbar riga yayin da suke rawan wakar Yarbawa ta Asake Omo Ope.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng