Allah ya azurta ma’auratan da suka yi shekaru 6 ba haihuwa da ‘yan uku shekaru 3 bayan sun karbi rikon wata yarinya
- Allah ya azurta Aminu da Hafsan da haihuwar ‘yan uku bayan shekaru shida da aurensu ba tare da samun ciki ba
- Ma’auratan sun karbi rikon wata yarinya mace mai suna Princess Zahra shekaru uku bayan aurensu saboda rashin haihuwa
- Aminu da Hafsat sun haifi yan uku duk maza a ranar Juma’a, 13 ga watan Nuwamba
Shekaru uku bayan sun karbi rikon wata yarinya, Allah ya azurta wasu ma’aurata wadanda suka yi shekaru shida da aure da haihuwar ‘yan uku.
A wani rahoto da shafin Northern Habiscus ta wallafa, ma’auratan masu suna Aminu da Hafsat sun karbi rikon wata yarinya sannan suka sanya mata suna Princess Zahra, saboda Allah bai basu haihuwa ba.
Sai gashi Ubangiji ya azurta su da haihuwar ‘yan uku duk maza shekaru uku bayan sun karbi rikon Princess Zahra.
KU KARANTA KUMA: Zunubina guda a PDP shine cewa na ki matsawa Buhari, Gwamna Umahi
Mai jegon ta wallafa a shafinta na soshiyal midiya:
"Alhamdulillah Alhamdulillah. Lallai Allah mai rahama ne. Allah ya azurtamu da yan uku maza, a ranar 13 ga watan Nuwamba 2020.”
Northern Habiscus da ke Instagram @northern_hibiscuss ta wallafa kyawawan hotunan ma’auratan da Princess Zahra a shafinta.
KU KARANTA KUMA: Ganduje: Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano ta fi kowacce tasiri a Nigeria
A wani labari na daban, Bashir El-Rufai, daya daga cikin yaran gwamnan jihar Kaduna, ya haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya bayan ya wallafa hotunansa da amaryarsa a kan Twitter.
A cikin hotunan, an gano Bashir rike da kugun amaryarsa yayinda ita ma ta kamo shi cike da kauna.
A wani hoto kuma, an gano Bashir yana sumbatar amaryarsa a kumatu yayinda ita kuma ta rike fuskarsa tana murmusawa.
Sai dai kuma hakan ya fusata musulmai da Hausawa da ke amfani da Twitter inda suka yi wa hakan kallon bai dace ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng