Shugaba Tinubu Ya Karya Bakin da Aka Yi wa Najeriya na Shekaru 60 a Bankin Duniya

Shugaba Tinubu Ya Karya Bakin da Aka Yi wa Najeriya na Shekaru 60 a Bankin Duniya

  • Wale Edun a matsayinsa na Ministan kudi da tattalin arzikin Najeriya, ya samu babban mukami a Bankin Duniya/IMF
  • Ministan zai rike wannan kujera na tsawon shekara guda kafin a zagaya da ita zuwa sauran kasashen da ke cikin nahiyar
  • Tun da ake a tarihi, mutumin Najeriya bai taba zama shugaban kungiyar gwamnonin Afrika ba sai a wannan karo

Morocco - Ministan da ke kula da kudi da tattalin arziki, Olawale Edun, ya ce Najeriya ta samu babban kujera a bankin Duniya/IMF.

Rahoto ya fito daga The Cable cewa kasar Najeriya ta samu shugabancin kungiyar gwamnonin Afrika a babban bankin Duniya.

Wale Edun ya ce wannan zai bada dama a hada kan kasashen nahiyar Afrika ta karkashin ministoci kudi da jagororin gwamnati.

Wale Edun
Wakilin Najeriya, Wale Edun a taron IMF/Bankin Duniya Hoto: @GreaterNgr
Asali: Twitter

Najeriya ta samu kujera a bankin Duniya

Kara karanta wannan

Masanan Duniya Sun Taimaki Tinubu da Muhimman Shawarwari da $1 ta Zarce N1000

Ministan ya yi maganar nan a ranar Talata wajen taron Bankin Duniya/Hukumar IMF na shekara-shekara wanda aka yi a Marrakech.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin jawabinsa a kasar ta Moroko, Ministan Najeriyan ya yi kira ga shugabannin Afrika su hada-kai domin ganin kowa ya ci riba.

"Yanzu Najeriya ta na da dama a matsayin shugabar kungiyar Gwamnonin Afrika, ta hada kan kasashen Afrika da murya guda."

- Wale Edun

An rahoto Mista Edun ya na mai cewa mukamin zai bada dama ga kasashen su rika magana da kalma daya a duk fadin Duniya yanzu.

Yadda aka kafa kungiyar gwamnonin

Wannan kungiya ta Bankin Duniya da Hukumar IMF mai bada lamuni ta na kunshe da Ministocin kudi da kuma gwamnonin babban banki.

Tsari da dokar IMF ta ba kowace kasar nahiyar damar fito da shugaban kungiyar, ana zagaya da kujerar nan ne ta jerin sunan kowace kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu Na Shawarar Kirkiro Kotun Musamman Domin Daure Barayin Gwamnati

Tsarin da aka bi wajen zagayawa da mukamin zai hana wata kasa ta iya rike kujeran sau biyu a lokacin da wasu kasashen ba su kai rike ba tukun.

Wale Edun zai yi shekara 1 a mulki

Jaridar ta ce a lissafin da ake kai, ya kamata Najeriya ta shugabanci kungiyar ne a 2026, bayan kasashen Cape Verde da Eriteriya a 2024 da 2025.

Sai dai Edun ya ce an ba kasarsa wanda ta fi kowa karfin tattalin arziki a Afrika damar a karon farko a tarihi, shugaba daya zai yi shekara a ofis.

Najeriya ta daina biyan tallafin fetur

Kwanaki an ji labari Mele Kyari ya yi bayanin yadda biyan tallafin fetur da ake yi, ya nemi ya durkusar da kamfanin NNPCL a kwanakin baya.

Wannan ya zama labari a halin da ake ciki, Malam Kyari ya ce nan gaba Najeriya za ta fara fita da mai da aka tace zuwa wasu kasashen Duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng