Yadda Mu Ka Je Makarantar Yauri, Mu Ka Yi Gaba da Yara a 2021 Inji ‘Dan Bindiga

Yadda Mu Ka Je Makarantar Yauri, Mu Ka Yi Gaba da Yara a 2021 Inji ‘Dan Bindiga

  • Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi namijin kokarin wajen cafko mutane sama da 50 da ake zargin sun aikata laifuffuka
  • A cikin wadanda aka kama akwai Auwal Abdullahi wanda ya ce da shi aka sace daliban makarantar FGC Yauri a shekarar 2021
  • ACP Muyiwa Adejobi ya ce kokarin dakarun DFI-IRT and DFI-STS ya sa sun gano makamai, waya da kuma wasu dalolin bogi

Abuja - Dakarun ‘yan sanda na IRT da ke aiki na musamman sun gabatar da mutane 54 da ake zargin masu laifi ne da ba su da gaskiya.

Daga cikin wadanda aka gabatar gaban duniya, Vanguard ta ce akwai Auwal Abdullahi wanda ya amsa laifin satar 'yan makaranta.

Auwal Abdullahi ya yi bayanin yadda shi da wasu ‘yan bindiga a 2021 su ka shiga makarantar gwamnati ta FGC Yauri a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

‘Yan Fashi Sun Yi Shigan ‘Yan Sanda, Sun Yi Satar Miliyoyin Kudi Ido Ya Na Ganin Ido

'Yan sanda
Rundunar 'Yan sanda sun kama ‘Dan Bindiga Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Garkuwa da daliban FGC Yauri

Wanda ake zargi yake cewa sun dauke yaran makarantar ne, su ka shiga da su jejin Dansadau da ke Zamfara, an yi haka ne tun a 2021.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wannan mutum, sun yi garkuwa da daliban ne da hadin-kan Kachala Dogo Gide. 'Yan sanda sun daura bidiyon a shafukansu.

Auwal Abdullahi ya ce Kachala Dogo Gide da wasu ‘yan bindiga kusan 100 su ka dura makarantar gwamnatin, su ka yi garkuwa da yaran.

Jami’an ‘yan sanda sun nuna cewa Kachala Dogogide ya na cikin shugaban gungun ‘yan bindiga, ya na da yara kusan 100 a karkashinsa.

'Yan sanda sun kama mai dalar bogi

Mai magana da yawun bakin ‘yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya ce daga cikin wadanda su ka kama har da wanda aka samu da Dalolin karya.

Kara karanta wannan

Malamin Makaranta Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa Bayan Ya Zane Ɗaliba Mace a Abuja

An rahoto ACP Muyiwa Adejobi ya na mai cewa rundunonin DFI-IRT da na DFI-STS sun karbe makamai 92 da harsashi masu ci akalla 760.

Baya ga Dalolin bogi $760, 000, ‘yan sandan sun samu wadanda ake tuhuma da laifi dauke da bama-bamai biyu da rigar kunan bakin wake.

IRT ta iya cafke mutane biyar da ake zargin su na da hannu wajen yin garkuwa da wani baturen kasar Switzerland mai suna Diego Tanner.

EFCC ta gano kudin sata

A bangare guda, rahoto ya zo cewa hukumar EFCC ta na binciken tsofaffin gwamnoni, wasu tsofaffin ministoci da manya a gwamnati.

Ana bincike a kan satar da aka tafka a ma’aikatar wuta da wajen sayen kayayyakin gona, an gano yadda aka karkatar da dalolin aikin Mambila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng