“Zan Biya Ka Sadakinka Idan Za Ka Iya Biyana Gamsar Da Kai Da Na Yi”, Matar Aure Ga Mijinta
- Wani dan kasuwa mai suna Yahaya Mohammed ya fada ma kotu cewa zai yi wa matarsa sakin da ta nema idan ta biya shi N160,000 da ya kashe mata
- Matar, Hauwa Hamza ta ce za ta biya kudin idan har mijinta Mohammed ya biya ta gamsar da shi da ta yi da kuma girkin da ta shafe shekaru tana yi masa a matsayin matarsa
- Tun farko Hauwa ta tunkari wata kotun Kubwa inda ta nemi a raba aurensu mai shekaru uku saboda mijinta baya kula da ita kuma baya ganinta da gashi
Wata matar aure mai suna Hauwa Hamza ta tunkari wata babbar kotu a Kubwa, babban birnin tarayya, inda ta nemi a raba aurenta da mijinta, Yahaya Mohammed.
Hauwa ta nemi a raba aurensu ne kan cewa mijinta Mohammed baya bata kulawa kuma baya ganin mutuncinta.
An dai kulla aure tsakanin ma'auratan biyu ne daidai da koyarwar addinin musulunci a shekarar 2020 kuma Allah bai basu haihuwa ba.
Zan sake ki idan kika biya ni N160,000 da na kashe maki, miji ga matarsa a kotu
Sai dai kuma, mijin wanda ya kasance dan kasuwa ya sanar da kotun cewar zai saki matar tasa idan har za ta biya shi N160,000 da ya kashe mata, Daily Nigerian ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mohammed ya ce:
"Idan tana son saki, sai ta aura mun sabuwar mata. Ina so matata ta biyani duk abun da na kashe mata a aurenmu.
"Na biya N60,000 a matsayin sadakin auren matata kuma na kashe N100,000 wajen siya mata kaya, na dage sai ta biyani gaba daya kudin."
Ka biyani gamsar da kai da na yi a aurenmu, matar aure ga mijinta
“Ba Ki Da Hankali Ne?” Wani Mutum Ya Kurma Ihu Bayan Ya Kama Mai Aiki Tana Wanke Masa Kayan Wuta Da Sabulu
A martaninta, mai karar ta ce idan har Musulunci ya daura mata alhakin sama wa mijinta sabuwar mata kafin ya sake ta, za ta aikata hakan.
Ta kara da cewar Mista Mohammed bai kashe mata abun da ya yi N160,000 ba, cewa sadakinta ya kasance N60,000 ne kacal, rahoton Daily Post.
Hauwa ta ce:
"Ba ni da N160,000 da zan ba shi, sai dai idan shima zai biyani gamsar da shi da na yi a lokacin aurenmu da kuma girkin da na yi masa tsawon shekaru."
Sai dai kuma, Mohammed ya ce idan mai karar ta yi ikirarin cewa ta gamsar da shi, shima ya dauki dawainiyar ciyar da ita da kula da jin dadinta a auren.
Alhalin kotun, Mai shari'a Mohammed Wakili, ya bayyana cewa bai dace a addinin Musulunci ba a ce sai wacce ake karar ta samawa wanda ake kara sabuwar mata kafin ya saketa.
Mista Wakili ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 17 ga Oktoba domin yanke hukunci.
“Tana yi mun barazana da rayuwa”: Magidanci ya nemi a raba aurensa mai shekaru 51
A wani labarin, mun ji cewa wani mutum mai suna Ojo Olaoye, ya roki wata kotun gargajiya da ke Oja Oba, Mopa a Ibadan, jihar Oyo da ta raba aurensa mai shekaru 51 da matarsa Janet Olaoye.
Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, Ojo ya zargi matar tasa da taurin kai, yawan fada, tashin hankali da yin barazana ga rayuwarsa.
Asali: Legit.ng