Ba zan taɓa yin arziki ba muddin ina tare da shi - Matar aure ta garzaya kotu

Ba zan taɓa yin arziki ba muddin ina tare da shi - Matar aure ta garzaya kotu

Kafila Ogunsina, mahaifiyar ƴaƴa huɗu a ranar Alhamis to roki wata kotun gargajiya da ke zamanta a Ile-tunrun, Ibadan ta raba aurenta da saboda mijinta "ƴa daƙile mata arziki a rayuwa".

Kafilat wacce ke ɗinki ta shaidawa kotu cewa tun bayan da ta auri Tafiya shekaru 12 da suka gabata duk wani hanyar arziki ya toshe mata.

"Tunda na shigo gidansa a matsayin matarsa, komai ya tsaya min cak. Ba na gaba, bana baya. Gashi sai duk ta ya ke kamar baiwa.

"Rafiu ya kuma lalata duk abinda na mallaka yayin da na shigo gidansa," a cewar Kafilat.

Na kasa aje komai a rayuwa tunda na aure shi - Matar aure ta garzaya kotu
Na kasa aje komai a rayuwa tunda na aure shi - Matar aure ta garzaya kotu. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Umar: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan sabon shugaban riko na EFCC

Da ya ke mayar da ba'asi a kotun, Rafiu ya roki kotu kada ta raba aurensa da matarsa amma bai musanta zargin da ta yi akansa ba.

Rafiu, mai sana'ar aikin gini, ya nemi kotu ta taya shi rokon alfarma wurin matarsa kada ta rabu da shi.

"Ranka ya daɗe, kada ka raba mu. Ita ce rayuwa ta, gashi kuma ta iya kula da gida sosai.

"Babu tabbas zan iya sake samun wata mace kamar ta," a cewar Rafiu.

Shugaban Kotun, Cif Henry Agbaje ya roki wacce ta shigar da ƙarar ta ƙara haƙuri da mijinta.

Agbaje ya umurci ma'auratan biyu su taho da ƴan uwansu kotu a zaman da za a sake yi.

Ya daga cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 13 ga watan Agustan 2020 don yanke hukunci.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Rundunar 'Yan sanda a jihar Abia ta kama wata Mrs Rose Uwaga a kan zargin sheke mijinta mai shekara 83, Alhaji Isa Uwaga a Umuahia babban birnin jihar.

Kakakin rundunar ta jihar, Geoffrey Ogbonnaya ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, kama matar mai shekaru 73 a garin Umuahia a ranar Laraba.

Ogbonnaya ya ce daya daga cikin yayan Uwaga, Ibeabuchi, ne ya kai wa 'yan sanda rahoto a kan lamarin a ranar 2 ga watan Yuli.

Ya ce an mika binciken zuwa sashin binciken manyan laifuka na 'yan sandan wato CID domin zurfafa bincike.

Ya kuma ce gawar mamacin tana dakin ajiye gawa na asibiti "inda ake sa ran gudanar da bincike a kan ta don sanin anihin abinda ya kashe mutumin."

NAN ta gano cewar ma'auratan sun samu rashin jituwa har ta kai ga dambacewa a gidan su da ke Ohobo-Afara Umuahia.

"Yayin fadar, mutumin ya dakko adda domin ya firgita matar amma ta fi karfinsa ta murde hannunsa.

"Addar ta fadi daga hannunsa kuma matar da ke da girman jiki ta danne shi a kasa ta shake masa wuya har sai da ya mutu," a cewar wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel