Saura Kiris Zuciyata Ta Buga da Na Ji Rade-Radin Mutuwar Gowon Inji Tsohon Minista

Saura Kiris Zuciyata Ta Buga da Na Ji Rade-Radin Mutuwar Gowon Inji Tsohon Minista

  • Cif Edwin Clark ya na jin rade-radin mutuwar Yakubu Gowon sun fara yawo a gari, sai ya kira wayar salular tsohon mai gidan shi
  • Janar Yakubu Gowon ya tabbatarwa dattijon Neje-Deltan cewa da ran shi, akasin yadda ake yadawa a kan shafukan sada zumunta
  • Edwin Clark ya yi aiki da tsohon shugaban Najeriyan a lokacin mulkin soja, ya rike masa ministan sadarwa har ya bar mulki a 1975

Abuja - A makon nan kurum aka fara yada wasu jita-jita cewa Yakubu Gowon ya rasu, ya bar duniya ya na mai shekara 88.

Daga baya aka tabbatar da cewa wannan labari bai da tushe, Janar Yakubu Gowon ya tabbatar da cewa ya na nan a raye har yau.

Edwin Clark wanda ya na da alaka mai kyau da tsohon shugaban na Najeriya ya ce jita-jitar ta kusa jefa shi a cikin matsala.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Yi Magana Kan Digirin Tinubu, Ya Fito da Takardun Karatunsa

Gowon
Yakubu Gowon tare da Olusegun Obasanjo Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Abin da Gowon ya fadawa Edwin Clark

The Cable ta ce da yake zantawa da ‘yan jarida ranar Talata a Abuja, Cif Edwin Clark ya ce saura kiris ya samu bugawar zuciya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A jiya dandalin sada zumunta ya kusa jawo mani bugun zuciya da su ka sanar da cewa Janar Yakubu Gowon ya tafi.
Na yi lilis sai kurum na gano ba gaskiya ba ne da na tuntubi Janar Gowon ta wayar salula
(Gowon) Ya ce mani ‘Ina nan a raye tukuna, har yanzu ina jin dadin kasar nan da kuma matsayin da na ke da shi."

- Edwin Clark

Shawarar Cif Edwin Clark ga al'umma

Da yake magana da ‘yan jarida a jiyan, Clark ya yi kira ga al’umma su zama masu gaskiya tare da mutunta duk wani ‘dan Najeriya.

Kara karanta wannan

Wahalar fetur: NNPC Ya Fadi Abubuwa 2 da Su ka Jawo Layin Mai a Garuruwa

Tsohon ministan sadarwan a lokacin mulkin sojoji yake fadawa manema labarai cewa a guji maida wasu saniyar ware a kasar nan.

Gowon ya yi mulki tsakanin Agustan 1966 zuwa watan Yulin 1975 lokacin da Marigayi Janar Murtala Mohammed ya kifar da shi.

Olusegun Obasanjo ya soki Buhari

Buhari wanda ya yi shekaru takwas ya na mulki ya na ikirarin gwamnatinsa ta bunkasa tattalin arziki, Olusegun Obasan ya na da ja.

Ana da labari Obasanjo ya zargi Muhammadu Buhari da ruguza tattalin arziki, ya jawo lissafin bashin da ake bin Najeriya ya dawo sabo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng