Masu Cin Gajiyar N-Power Sun Koka da Rashin Biyansu Hakkinsu Har Na Tsawon Watanni 10

Masu Cin Gajiyar N-Power Sun Koka da Rashin Biyansu Hakkinsu Har Na Tsawon Watanni 10

  • Masu cin gajiyar shirin N-Power sun koka kan yadda aka dakatar da shirin lokaci guda duk da dumbin basuka da su ke bi
  • Gwamnatin Tarayya dai ta sanar da dakatar da shirin wanda tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta kirkiro saboda wasu matsaloli
  • Legit Hausa ta tattauna da wasu shugabannin masu cin gajiyar a jihar Gombe inda su ka bayyana damuwa kan tsarin shirin

Jihar Gombe - Yayin da gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin N-Power, masu cin gajiyar shirin sun koka ganin yadda aka rusa shirin a lokacin da aka fi bukata.

Wasu da Legit Hausa ta tattauna da su kan dakatar da shirin sun bayyana kaduwarsu ganin yadda su ke bin gwamnatin bashi na watanni da dama.

Masu cin gajiyar N-Power aun bukaci gwamnati ta biya su kudadensu
Masu Cin Gajiyar N-Power Sun Tura Sako Ga Gwamnatin Kan Basuka. Hoto: Betta Edu, Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Meye jama’a ke cewa kan dakatar da shirin N-Power

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Musulunci Yayin Da Su Ke Raka Gawa Makabarta, Bayanai Sun Fito

Shugaban masu cin gajiyar a Gombe, Kwamred Imran Hassan Ajiya ya ce a gaskiya abin bai yi dadi ba saboda ya kamata a biya kudaden da aka riga aka yi aiki kafin dakatarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce daman sun riga sun sani idan sabuwar gwamnati ta zo dole za ta iya sauya tsare-tsaren da ke cikin shirin inda ya ce shi ma ya na bin bashi har na tsawon watanni tara.

Ana shi martanin, Sakataren kungiyar ta kasa, Kwamred Bashir Ladan ya ce gaskiya ba su ji dadi ba da aka dakatar da shirin ganin irin wahalhalun da su ka shiga lokacin dibansu.

Wane sako su ka tura kan dakatar da shirin N-Power?

Ladan ya ce wannan abu ne na ‘yan siyasa, an yi ta mana alkawura amma daga baya aka ce za a fara bincike inda a karshe aka dakatar da shirin gaba daya.

Kara karanta wannan

Seyi Tinubu Ya Jawowa Mahaifinsa Suka Saboda Yawo a Jirgin Shugaban Kasa

Ya kara da cewa zai yi wahala a dawo da shirin ganin yadda tun farko babu tsari a cikinsa.

Kwamred Adamu M. Haram wanda ya kasance mataimakin shugaban kungiyar a jihar Gombe, ya koka kan yadda aka dakatar da shirin a dai-dai wannan lokaci.

Ya ce shi kansa ya na bin bashi har na tsawon watanni goma yayin da wasu ke bin watanni tara.

Haram ya ce kamata ya yi kafin a dakatar da shirin a tabbatar an gama biyan basukan da mutane ke bi, idan ya so duk matakin da za a dauka sai a dauka.

A karshe ya shawarci matasa masu cin gajiyar musamman a asibitici da makarantu da su ci gaba da zuwa aiki don taimakon al’umma.

Kokarin jin ta bakin shugaban masu cin gajiyar na kasa da mataimakinsa ya ci tura bayan rashin samun damar daga kirar waya da wakilin Legit Hausa ya musu.

Kara karanta wannan

A Yi Gaba a Dawo Baya: Tinubu Ya Dawo fa Shirin Buhari Na 'Tradermoni', Ya Bayyana Kudaden da Za a Samu a Shirin

Tinubu ya dakatar da shirin N-Power saboda wasu matsaloli

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin N-Power a kasar har sai baba-ta-gani saboda matsalolin da ke kunshe a cikin shirin.

Ministar Jin Kai da Walwala, Dakta Betta Edu ita ta bayyana haka inda ta ce za su gudanar da bincike kan batan wasu makudan kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.