Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Dan Nijar Da Zargin Safarar Makamai A Jigawa
- Jami’an ‘yan sanda a jihar Jigawa sun kwamushe wani dan Nijar da wasu mutum biyar kan zargin safarar makamai
- Kakakin rundunar a jihar, ASP Abubakar Sadik ya ce an kama dan Nijar din ne Bilal Faraji mai shekaru 29 bayan samun bayanan sirri
- Har ila yau, rundunar ta kuma kama wasu mutane uku kan zargin fasa filin jirgin sama tare da yin sata
Jihar Jigawa – Rundunar ‘yan sanda a jihar Jigwa ta cafke wani dan Nijar kan zargin safarar muggan makamai da kuma satar babur.
Wanda ake zargin, Bilal Faraji mai shekaru 29, an kama shi ne da wasu ‘yan Najeriya su biyar, cewar Punch.
Waye 'yan sanda su ka kama da makamai a Jigawa?
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, ASP Abubakar Sadiq ya tabbatar da kama wadanda ake zargin a yau Laraba 4 ga watan Oktoba a Dutse.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce sauran wadanda aka kaman akwai Yusuf A. Yusuf mai shekaru 28 da ke karamar hukumar Kazaure da ke jihar Jigawa.
Sadiq ya ce dukkan wadanda aka kaman ana zarginsu da safarar muggan makamai ga ‘yan bindiga da su ka addabi yankin Ringim da sauran kewaye.
Ya kara da cewa a yayin bincike, sun tabbatar da cewa su na siyarwa tare da safarar makamai zuwa jihohin Kano da Jigawa.
Rundunar ta ce an kama su ne bayan samun bayanan sirri inda ake zargin sun fasa wani gida a ranar 28 ga watan Satumba, Platform Times ta tattaro.
Ya ce:
“Wani mai suna Sagiru Musa da ke zaune a kauyen Kakikankare a karamar hukumar Ringim ya kawo rahoton mutane hudu da su ka shiga gidansa da makami.
“Mutanen sun sace mota kirar ‘Golf 3 Wagon’ mai launin kore dauke da lamba kamar haka RNG 691 AA jihar Jigawa.”
An kuma kama wasu da zargin sata a filin jirgi
Har ila yau, bayan satar motar da aka kawo kara, sun kuma sace wayar salula karama kirar ‘Tecno, Gistlover ta tattaro.
Rundunar ta ce ta kuma kama wasu mutane uku kan zargin fasa filin jirgin sama tare da satar na’aurar sanyaya daki da lalata manyan wayoyin wutar lantarki.
Kakakin rundunar ya bayyana wadanda aka kaman kamar haka: Mutari Idris da Adamu Idris da Yasir Ilyasu.
'Yan sanda sun cafke mutum 14 kan zargin satar mazakuta
A wani labarin, Rundunar 'yan sanda a birnin Abuja ta kama mutane 14 kan yada karya na satar mazakuta.
Rundunar ta ce ta kama mutanen ne bayan kwakkwaran bincike da ya tabbatar karya su ke.
Asali: Legit.ng