Kungiyar NLC Ta Ce Mafi Karancin Albashi Nan Gaba Zai Kai N100,000 Zuwa N200,000

Kungiyar NLC Ta Ce Mafi Karancin Albashi Nan Gaba Zai Kai N100,000 Zuwa N200,000

  • Shugaban Kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajaero ya bayyana cewa mafi karancin albashi zai kai dubu 100 zuwa 200 nan gaba
  • Ajaero ya bayyana haka ne a yau Talata 3 ga watan Oktoba yayin hira da gidan talabijin na Channels a Abuja
  • Ya ce nan gaba kadan za su fara tattaunawa da gwamnati kan sabon mafi karancin albashi ga ma’aikata ganin halin da ake ciki

FCT, Abuja Kungiyar Kwadago a Najeriya (NLC) ta bayyana yawan adadin mafi karancin albashi da za su tattauna da Gwamnatin Tarayya a nan gaba.

Kungiyar ta ce akalla gwamnatin sai ta biya Naira dubu 100 zuwa 200 a matsayin mafi karancin albashi ganin yadda komai ke tsada.

'Mafi karancin albashi zai kai dubu 100 zuwa 200'. NLC
Kungiyar NLC Ta Bayyan Mafi Karancin Albashi Nan Gaba. Hoto: Bola Tinubu, Joe Ajaero.
Asali: Facebook

Meye kungiyar NLC ta ce kan mafi karancin albashi?

Kungiyoyin kwadago sun shirya shiga yajin aiki a yau Talata 3 ga watan Oktoba bayan cire tallafin mai a kasar.

Kara karanta wannan

Abin da Zai Faru Nan da Kwana 30 Idan Gwamnati ta Karya Alkawarinmu - ‘Yan Kwadago

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani su ka janye bayan sun yi wata ganawa da Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin 2 ga watan Oktoba a Abuja.

Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero ya ce sun daga yajin aikin ne don bai wa gwamnatin lokaci don cika alkawuran da ta dauka, New Telegraph ta tattaro.

Ya ce daga alkawuran akwai Naira dubu 35 da za ta kara wa ma’aikata a matsayin rage radadin cire tallafi inda ya ce mafi karancin albashin na iya kai wa Naira dubu 200.

Ya ce:

“Wannan ba mafi karancin albashi ba ne, amma an kara ne kawai don rage radadi, a watan Maris ko Afrilu za mu tattauna sabon mafi karancin albashi wanda zai kai dubu 100 zuwa 200.

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu mutane kan maganar NLC:

Wani lakcara a Kwalejin Ilimi ta Tarayya mai suna Mohammed Abdullahi ya ce:

Kara karanta wannan

Yajin-Aiki: Tinubu Ya Karawa Ma’aikata N10, 000 a Yunkurin Lallabar ‘Yan Kwadago

"Ai daman tun da mu ka bari tsoffin gwamnoni ke jagorancinmu dole za mu ga abin da bai dace ba da rashin adalci."

Ya ce babu abin da NLC za ta yi sai kare aljihunta.

Yusuf Muhammad daga Gombe ya ce:

"Mutane su na ba ni mamaki da su ke tunanin NLC na yi ne don talakawa, to ya labarin ma'aikatan jiha da kananan hukumomi."

Imran Muhammad ya ce:

"Ina labarin talakan da ba ya aikin gwamnati? shikenan shi kam ba dan kasa ba ne."

Aisha Hussaini ta ce wannan abin a yaba ne ganin yadda ake cikin tsadar rayuwa a Najeriya, kudaden za su taimaka sosai.

Wane tabbaci NLC ta bayar kan mafi karancin albashi?

Ajaero ya bayyana haka ne a yau Talata 3 ga watan Oktoba yayin hira da gidan talabijin na Channels.

Ya bayyana cewa wannan dubu 35 da aka kara an dora shi ne kan mafi karancin albashi na da na Naira dubu 30 inda ya ce za su duba abubuwa da dama yayin tattauna sabon mafi karancin albashi.

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

Ya kara da cewa:

“Akwai abubuwa da dama da za a duba yayin sabon mafi karancin albashi wanda su ka hada da tashin farashin kaya da sauransu.”

NLC ta fasa yajin aiki

A wani labarin, Kungiyar NLC ta fasa shiga yajin aikin da ta yi niyya a yau Talata 3 ga watan Oktoba.

Kungiyar ta umarci ma’aikata su koma ofis bayan wata tattaunawa da su ka yi da Gwamnatin Tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.