Yadda Dan Najeriya Da Ke Tuka Baro a Kasuwa Ya Zama Farfesa

Yadda Dan Najeriya Da Ke Tuka Baro a Kasuwa Ya Zama Farfesa

  • Nicholas Asogwa, lakcara a jami'ar UNN, ya ba da labarin yadda ya fita daga talauci ya zama farfesa da taimakon kwastamominsa biyu da suka dauki nauyin karatunsa
  • Asogwa yana sana'ar tura baro da gyaran takalma a jami'ar kafin Nkechi Ohanuka ta siya masa takardar JAMB sannan Proscovia Ndoboli ta biya masa kudin makarantarsa na farko
  • Asogwa ya sake haduwa da wadanda suka taimaka masa a 2013 sannan ya gode masu da iyayensa kan gudunmawa da karfafa masa gwiwa da suka yi

Wani malamin jami'ar Najeriya ya ba da labarin yadda ya fara daga matukin baro da gyaran takalmi zuwa farfesa a fannin da'a a jami'ar Najeriya, Nsukka (UNN).

Nicholas Asogwa, wanda ke karantarwa a bangaren Falsafa, ya samu karin girma zuwa matsayin Farfesa a ranar Talata, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

Ya ba da labarin rayuwarsa a cikin wata takarda mai taken "Gwagwarmayata zuwa matakin farfesa" wanda ya karanto a wajen wani taro da aka yi don karrama shi.

Daga tuka baro ya zama shahararren Farfesa
Yadda Dan Najeriya Da Ke Tuka Baro a Kasuwa Ya Zama Farfesa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Asogwa ya ce an haife shi a gidan da ke fama da "tsananin talauci" wanda ya zamo barazana ga damar da yake da shi na yin karatu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ya tuka baro a kasuwar Orie Orba da ke karamar hukumar Udenu ta jihar Enugu sannan ya yi gyaran takalma a daya daga cikin dakunan kwanan dalibai (Bello Hall) a jami'ar UNN domin samun na dogaro da kai.

Ya ce rayuwarsa ta canja ne lokacin da wasu kwastamominsa biyu, wadanda suka kasance daliban UNN suka taimaka masa wajen samun ilimin jami'a.

Daya daga cikinsu, Nkechi Ohanuka, lauya daga jihar Imo ta siya masa fom din JAMB don samun shiga jami'a. Dayar, Proscovia Ndoboli, daga Uganda ta biya masa kudin makarantarsa na farko sannan ta saka shi a dakin kwanan dalibai.

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

"Daga haka na fara. Nkechi ta siya min fom din JAMB, yayin da Proscovia ta biya kudin makarantata ta farko ta sanya ni a dakin kwanan dalibai. Daga nan ne ni da iyayena suka ci gaba, aka ci gaba da gwabzawa,” inji shi.

Asogwa ya ce ya rasa hanyar hulda da matan biyu tsawon shekaru har sai da ya sake haduwa da su ta Google da Facebook a 2013, jim kadan bayan ya kammala Ph.D dinsa.

Ya nuna godiya garesu da iyayensa, wadanda suka cusa masa darajar ilimi da yarda da aiki tukuru da jajircewa.

Ya ce yana fatan labarinsa ya zaburar da sauran mutane da ke fuskantar kalubale irin nasa sannan ya karfafa masu gwiwar kada su yanke kauna da mafarkinsu.

Matashi ya nunawa duniya sauyawar yarinyar da ya tsinta a bola, ta fara makaranta

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya da ya tsinci yarinya a bola watanni da suka gabata ya yi karin haske kan rayuwar yarinyar.

Bawan Allah mai suna, Ben Kingsley Nwashara, ya tsinci yarinyar da wata da ba a san kowacece ba ta yasar sannan ya dunga kula da ita tun daga lokacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng