Kungiya Ta Umarci Ma’aikatanta Su Tafi Ofis a Yau, NLC da TUC Sun Fasa Yajin-Aiki

Kungiya Ta Umarci Ma’aikatanta Su Tafi Ofis a Yau, NLC da TUC Sun Fasa Yajin-Aiki

  • Kungiyar MWUN ta aikawa ma’aikatanta sanarwa cewa su jinginar da batun shiga yajin-aiki
  • Kwamred Prince Adewale Adeyanju ya tabbatar da sulhun gwamnati da shugabannin NLC da TUC
  • Kennedy Ikemefuna ya fitar da sanarwa ta musamman bayan an hakura da tafiya yajin-aikin

Abuja - Shugabannin kungiyar MWUN ta ma’aikatan kan teku ta umarci ‘ya ‘yanta su koma bakin-aiki domin ba za a shiga yajin-aiki ba.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa kungiyar ta lashe aman da ta yi na shirye-shiryen tafiya yajin-aiki kamar yadda NLC da TUC su ka shirya.

A baya an ji MWUN ta yi umarni a rufe duk wasu wuraren ayyukan mai, kafofi da tashoshin teku da wadanda ke bakin ruwa a kasar nan.

Yajin-Aiki
Ma'aikata ba za su shiga yajin-aiki ba Hoto: maintenanceandcure.com
Asali: UGC

"Babu yajin aiki" - Prince Adewale Adeyanju

Shugaban kungiyar MWUN na kasa, Prince Adewale Adeyanju, ya fitar da takarda a daren yau, ya na cewa an iya sasantawa da gwamnati.

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamred Prince Adewale Adeyanju ya tabbatar da ba za a shiga yajin-aikin da aka yi niyya ba.

NLC da TUC sun sasanta da gwamnati

Abin da rahoton ya nuna shi ne an cin ma matsaya a lokacin da aka yi wani zaman gaggawa tsakanin jagororin kwadago da gwamnati.

Shugabannin NLC da TUC sun amince su janye yajin-aiki domin a aiwatar da bukatun da su ka gabatar a sakamakon cire tallafin man fetur.

Adeyanju ya ce majalisar kolin NLC ta umarci duka ‘ya ‘yanta su tafi aiki a maimakon a shiga yaji, 'Yan kwadago sun janye yajin da wata guda.

A jawabin da Kwamred Kennedy Ikemefuna ya sa hannu, MWUN ta ce kungiyoyin kwadago da na ‘yan kasuwa sun dakatar da yajin-aiki.

Kennedy Ikemefuna wanda shi ne shugaban yada labarai na kungiyar ma’aikatan tekun ya nuna Prince Adeyanju ya yi umarni a kama aiki.

Kara karanta wannan

Yajin-Aiki: Tinubu Ya Karawa Ma’aikata N10, 000 a Yunkurin Lallabar ‘Yan Kwadago

Wannan ya tabbatar da zaman da aka yi da kungiyoyin ma’aikata a ranar Litinin ya yi tasiri.

Za a biya ma'aikata N35,000

A baya an samu labari Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin kudi a kan alawus da za a rika biyan ma’aikatan gwamnati saboda tsadar fetur.

A maimakon N25, 000, gwamnatin tarayya ta amince a rika biyan N35, 000 na watanni shida, da alama ma'aikata sun amince da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng