APC Ta Bayyana Matsayar Tinubu Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur

APC Ta Bayyana Matsayar Tinubu Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur

  • Jam’iyyar APC ta musanta batun cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta mayar da tallafin man fetur a fakaice
  • Felix Morka, kakakin jam'iyyar APC, ya ce kalaman da hadimin Atiku ya yi na cewa Tinubu ya kashe N169.4bn domin tallafin man fetur a watan Agusta, ba gaskiya ba ne
  • A cewar Morka, shiga tsakani da gwamnati ta yi na daidaita farashin man, bai kai ga dawo da tallafin man fetur ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da iƙirarin cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sake ɓullo da tallafin man fetur ta bayan fage, inda ta ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta shiga tsakani ne kawai don daidaita farashinsa.

A kwanakin baya ne dai aka samu rahotannin cewa Shugaba Tinubu a watan Agusta ya amince da kashe kuɗi N169.4bn domin farashin man fetur ya tsaya a kan N620, cewar rahoton Business Day.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Za Su Fara Siyan Litar Fetur Kan Naira 180" Malami Ya Hango Sauki, Ya Fadi Lokaci

APC ta musanta batun dawo da tallafin man fetur
APC ta yi magana kan batun dawo da tallafin man fetur Hoto: APC Nigeria
Asali: Twitter

APC ta yi bayani kan ₦169.4bn da aka kashe a watan Agusta

Jam’iyyun adawa sun caccaki gwamnatin Tinubu kan dawo da tallafin man fetur ta hanyar bayan fage, amma jam’iyyar APC a daren ranar Litinin, 25 ga watan Satumba, ta ce ƙoƙarin daidaita farashin bai kai ga ace an sake dawo da tallafin man fetur ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Phrank Shaibu, hadimin Atiku kan harkokin watsa labarai, ya yi iƙirarin cewa Shugaba Tinubu ya mayar da tsarin tallafin man fetur ta bayan fage.

APC ta caccaki mai taimaka wa Atiku

Sai dai, a wata Felix Morka, kakakin jam'iyyar APC na ƙasa ya fitar, ya bayyana cewa:

"Iƙirarin Shaibu na cewa tallafin man fetur ya dawo ba daidai ba ne. Shigar da gwamnati ta yi don tabbatar da daidaituwar farashin da abin da ka iya zuwa ya dawo, bai kai ga dawo da ɓarnar tallafin man fetur ba da aka yi a baya."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Gobarar Kotun Koli, Ta Bayyana Abinda Take Zargi

Felix Morka, ya ƙara da cewa kalaman Shaibu yaudara ce bayan ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu na tafiyar da ƙasar nan a kan farfaganda.

NNPC Na Bin Tinubu Bashin Tiriliyan 7.3

A wani labarin kuma, kamfanin man fetur na ƙasa ya bayyana cewa ya biyo gwamnatin tarayya bashin tiriliyan 7.3 na tallafin man fetur.

Kamfanin ya ce gwamnatin ta rike Naira tiriliyan 4.1 inda ta kuma ta gaza tura Naira tiriliyan 2.8 zuwa ga asusun Gwamnatin Tarayya yayin da ta kuma rike wa kamfanin Naira tiriliyan 1.3.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel