Hukumar FCTA Za Ta Fara Kama Fasinjoji Don Dakile Harkar Achaba A Abuja

Hukumar FCTA Za Ta Fara Kama Fasinjoji Don Dakile Harkar Achaba A Abuja

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike na ci gaba da inganta birnin Abuja bayan hukumomi sun kama masu babura a birnin
  • Hukumar FCTA ta bayyana cewa za ta fara kama fasinjoji ma su hawa babura don dakile aikin achaba a birnin gaba daya
  • Har ila yau, hukumar ta lalata babura 478 da aka kama a wuraren da aka haramta aikin achaba a birnin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Hukumar Gudanarwa ta Abuja (FCTA) ta bayyana cewa za ta fara kamen fasinjojin da su ke hawa achaba.

Hukumar wacce ke karkashin jagorancin ministan Abuja, Nyesom Wike ta ce idan ta kama fasinjoji ma su hawa achaba dole su bar aiki a birnin.

Wike ya lalata babura 478, zai fara kama fasinjoji
Hukumar FCTA Za Ta Fara Kama Fasinjojin Da Ke Hawa Babura. Hoto: Nyesom Wike, FCTA.
Asali: Facebook

Meye Wike ya ce kan masu babura a Abuja?

Har ila yau, hukumar ta lalata babura 478 da aka kama su na achaba a wuraren da aka haramta achaba da sauran wurare, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Rundunar Tsaro Ta Bayyana Dalili 1 Tak Da Ke Hana Su Kawo Karshen Rashin Tsaro, Ta Yi Bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun bayan hawan Wike minista ake ta faman kawo sauye-sauye don inganta birnin Abuja.

Akalla an shafe makwanni biyu ana wannan aiki inda gamayyar jami'an tsaro gaba daya ke sintiri don kama babura a cikin birnin da Lugbe da kuma Kubwa.

Daraktan daya daga cikin hukumomin da su ke wannan sintiri, Bello Abdulateef ya shawarci jama'a da su rinka takawa da kafa a makusantan wurare don tsaron kansu da lafiya.

Wane shawari hukumar ta bai wa 'yan achaba a Abuja?

Ya ce:

"Ko dan tsaron kansu da lafiya, mutane su guji hawa babura saboda za mu fara kama su a matsayin fasinjoji."

Bello ya ce sun haramta yin achaba a birnin Tarayya Abuja saboda tsaro da kuma lafiyar jama'a, Independent ta tattaro.

Ya kara da cewa dokar ta shafi yankunan da ke kusa da Abuja saboda su ma bai kamata ana achaba ba don dalilin lafiya da kuma tsaron al'umma.

Kara karanta wannan

Auren Sadiya Haruna Da G-Fresh Ya Shiga Tangal-Tangal, Rigima Ta Kai Gaban Alkali

Ya shawarci ma su sana'ar achaba da wadanda su ke kasuwancin babura da su sake lale saboda hukumar ba za su daga musu kafa ba.

Legit Hausa ta zanta da wasu kan wannan lamari:

Abubakar Aminu ya ce:

"Wallahi wannan zalunci ne Allah ya bi musu kadunsu, ya kamata gwamnati ta duba halin da ake ciki.

Yayin da Ja'afar Salaf ya ce abun da ya ke shirin yi ba zai yiyu ba, ta yaya za a kama ma su hawa babura kuma.

Muhammad Hassan ya ce:

"Maganin mutane kenan lokacin da mu ke cewa ga Atiku su na yaudarar ku da wani abu daban."

Wike ya tsare wasu matasa da ke hayaniya kusa da gidansa

A wani labarin, Jami'an tsaro sun cafke wasu matasa da ke yin hayaniya kusa da gidan ministan Abuja, Nyesom Wike.

Tuni aka tura matasan gaban kotu inda alkalin kotun ya ce sai iyayensu sun zo za a ba da belinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.