Farfesa Osinbajo Ya Samu Babban Mukami A Hukumar Yanayi Ta Afirka
- Farfesa Yemi Osinbajo ya samu babban mukami a Hukumar Yanayi a Nahiyar Afirka wanda zai jagoranta
- Farfesan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Laraba 27 ga watan Satumba inda ya ce ya yi matukar murna
- Wannan shi ne mukami na biyu da tsohon mataimakin shugaban kasar ya samu bayan barinshi ofis a watan Mayu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya samu mukami a hukumar Yanayi ta Afirka.
Osinbajo ya samu mukamin ne a matsayin shugaban Hukumar Yanayi ta Afirka (CAP-A), Legit ta tattaro.
Wane mukami Osinbajo ya samu karo na biyu?
Farfesan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Laraba 27 ga watan Satumba inda ya ce ya yi matukar murna da samun mukamin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya rubuta kamar haka:
“Ina murnar samun wannan mukamin da na karba na jagorantar Hukumar Yanayi a Afirka (CAP-A), za mu kawo sauyi a bangaren yanayi da jajirtattun abokan aiki.
Wannan mukami na Osinbajo shi ne na biyu tun bayan barin ofishi a matsayin mataimakin shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.
Wane mukami Osinbajo ya fara samu?
A farkon watan Yuli, Osinbajo ya samu mukamin mai ba da shawara na musamman a hukmar makamashi da harkokin jama'a (GEAPP).
Hukumar ta sanar da mukamin nashi ne a ranar Talata 11 ga watan Yuli a yanar gizonta.
Farfesa Osinbajo ya kasance tsohon mataimakin shugaban kasa a mulkin Muhammadu Buhari na wa'adi biyu da su ka yi daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Osinbajo shi ne ya ke jagorantar Kwamitin Tattalin Arziki (NEC) a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Buhari.
Gwamnan APC Ya Yi Magana Mai Kyau Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a Zaɓen 2023
Ya kuma rike bangaren tsare-tsaren kudade da ba da tallafi na 'Trader Money' a lokacin da su ke kan mulki.
Osinbajo ya samu sabon mukami bayan barin ofis
A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya samu sabon mukami makwanni shida bayan barin ofis a watan Mayu.
Osinbajo ya samu mukamin ne a kamfanin Global Energy Alliance for People and Planet a matsayin mai ba da shawara na musamman.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka a ranar Talata 11 ga watan Yuli a shafinsa na Twitter.
Asali: Legit.ng