Tsohuwar Minista, Sadiya Farouk Ta Shiga Gangamin Ceto Daliban Da Aka Sace A Zamfara
- Yayin da ake jimamin sace dalibai a Zamfara, manyan mutane sun fara shiga gangamin neman sakin daliban
- Tsohuwar ministar Jinkai da Walwalar Jama'a, Sadiya Farouk ta bayyana kaduwarta da jin wannan lamari
- Sadiya ta bayyana haka ne a jiya Lahadi 24 ga watan Satumba a shafinta na Twitter inda ta yabawa jami'a tsaro
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Zamfara - Tsohuwar ministar Jinkai da Walwalar Jama'a, Sadiya Umar Farouk ya shiga jerin masu alhini kan sace dalibai a Zamfara.
Tsohuwar ministar ta bukaci gwamnati ta yi gaggawan ceto daliban da aka sace a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a jihar.
Meye Sadiya ta ce kan sace dalibai a Zamfara?
Farouk ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter a jiya Lahadi 24 ga watan Satumba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba a mantaba a ranar Juma'a ce 22 ga watan Satumba, 'yan bindiga su ka sace dalibai akalla 24 dukkansu mata a dakunan daliban.
Daga bisani jami'an tsaro sun kwato wasu daga cikin daliban da kuma ma'aikatan gini a jami'ar.
Wannan na zuwa bayan sake sace wasu daga cikin ma'aikatan gini a jami'ar su guda tara.
Saboda nuna goyon baya, mutane da dama a Najeriya sun fara gangami a kafafen sadarwa da don kwato daliban.
Yayin da ta ke martani, Sadiya Farouk ta bayyana sace daliban a matsayin abin takaici.
Sadiya ta nuna takaicinta game da sace daliban a Zamfara
Ta ce:
"Ina mika ta'aziyya ga 'yan uwa da iyalan wadanda aka sacen a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau, na yi matukar kaduwa da jin haka.
"Ina addu'ar dawowar daliban cikin koshin lafiya, ya kamata mu zama tsintsiya madaurinki daya a wannan lokaci.
"Ina yabawa jami'an tsaro kan kokarinsu na kwato wasu daga cikin daliban."
An sace dalibai 24 a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Zamfara
A wani labarin, 'yan bindiga sun sace dalibai 24 dukkansu mata a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau a cikin jihar Zamfara.
Rahotanni sun tabbatar da cewa zuwa yanzu jami'an tsaro sun kwato da yawa daga cikin wadanda aka sacen a ranar Juma'a 22 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng