Matsin Rayuwa: Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bukaci Malaman Musulunci Da Su Daina La'antar Shugabanni
- An yi kira ga malaman addinin Musulunci da su daina la'antar shugabanni saboda mawuyacin halin da ake ciki a kasar
- Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ne ya yi wannan kira inda ya bukaci malaman musulunci da su daina wa'azin da ka iya tunzura jama'a da kawo karan tsaye ga zaman lafiya
- Shehin Malamin ya bukaci yan Najeriya da su koma ga Allah don shine mai bayar da jin dadi a rayuwa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, ya yi kira ga malaman addini a kasar da su guji yin kalaman da ka iya haddasa rikici da barazana ga zaman lafiya a tsakanin Musulmai a kasar.
Ibrahim, wanda ya kasance babban dan jagoran Darika, Sheikh Dahiru Bauchi, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 23 ga watan Satumba, yayin da yake jawabi ga taron manema labarai a Bauchi daga cikin shirye-shiryen da suke yi na bikin Maulidi.
Ya roki mutane, musamman Malamai da su daina yi wa juna raddi a wajen wa’azi, rahoton Daily Trust.
A cewar Shehin malamin, galibin kiyayyar da ke tsakanin malaman addini ta samo asali ne daga hare-haren fatar baki da ake yi wa fahimtar juna, rahoton Nigerian Tribune.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shehin malamin ya bayyana cewa fahimtar juna da koyi da daddadiyar al'adun zaman lafiya da juna wajibi ne domin tabbatar da zaman lafiya a cikin al'umma.
Ku daina zagin malamai saboda halin da ake ciki, Sheikh Ibrahim ga yan Najeriya
Sheikh Ibrahim ya kuma bukaci yan Najeriya da su daina zagin shugabanninsu saboda halin kuncin da kasar ke ciki.
Ya bukaci yan Najeriya da su koma ga Allah da kyautata zaton cewa abubuwa za su gyaru, yana mai jaddada bukatar hakuri, da addu’a, da kuma halastattun hanyoyin kawo sauyi mai kyau.
Malamin addinin ya kuma jaddada muhimmancin nisantar cin zarafi ko la'antar shugabanni da manyan malamai, domin hakan ya saba wa koyarwar Musulunci.
Sheikh Ibrahim ya jaddada muhimmancin hadin kai, sannan ya bukaci al’ummar musulmi da su gudanar da ayyukansu na addini kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, tare da gudun abubuwan da ka iya raba kan al’umma.
Ya ce:
"Kangin rayuwa ko jin dadi duk daga Allah madaukakin sarki ne; abun da ya kamata yan Najeriya su yi a wannan lokaci shine komawa ga Allah sannan su nuna yakinin cewa abubuwa za su inganta."
Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wani malami mai suna Malam Shamsudeen Mahi dangane da abun da ya sa ake yawan samun sabani tsakanin malamai, inda ya ce:
"Yawancin lokuta abun da ke sa ake samun sabani shine banbancin akida, maimakon kowa ya bi abun da ya yarda da shi ba tare da kushe akidar wani ba sai ka ga kowa na son nuna lallai nasa ne daidai sannan na waninsa baya bisa kan tafarki.
"Amma idan har za a zauna ba tare da wani ya kushe wani ba toh a a samu aman lafiya. Ko Annabi ya yi rayuwa da kafirai ba tare da cutarwa ba, ya nemi su yi nasu addinin shima ya yi nashi wanda hakan ba karamin zaman lafiya ya haifar ba. Ta wannan dalilin ne ma wasu suka karbi addinin Musulunci.
"Ina kira ga yan uwana da mu yi addini ba tare da gaba ba sannan mu zauna lafiya a tsakaninmu ba tare da cin mutunci ko muzanta wani ba."
"Sannan la'antar shugabanni bai dace da mu ba saboda mafi yawancin lokuta mu ke jawo wa kanmu musiba da bakunanmu. La'antar shugabanni baya cikin koyarwar addini kamata ya yi a kodayaushe a cikin kowani hali mu taya shugabanninmu da addu'a domin ubangiji ya yi masu jagoranci."
Akwai alamun tambaya kan wasu yan siyasa game da kashe-kashen Filato, Mutfwang
A wani labari na daban, gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ce wasu ‘yan siyasa na da tambayoyin da za su amsa dangane da kashe-kashen da ake yi a jihar.
Caleb Mutfwang ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa kan matsalar tsaron da ya addabi jiharsa a wata hira da gidan talabijin na Channels TV cikin shirin Politics Today.
Asali: Legit.ng