Obasanjo Ya Karyata Bidiyon Da Ke Nuna Cewa Ya Sanya Labule Da Tinubu

Obasanjo Ya Karyata Bidiyon Da Ke Nuna Cewa Ya Sanya Labule Da Tinubu

  • Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana faifan bidiyo da aka ce ya gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a matsayin na bogi ne
  • Obasanjo ya yi Allah-wadai da bidiyon inda ya ce ya je ƙasar Afirka ta Kudu domin jana’izar fitaccen dan siyasar Ƙasar, Yarima Mangosuthu Buthelezi da za a yi a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba.
  • Obasanjo a ranar 1 ga watan Janairu, 2023, ya nuna amincewarsa ga ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi, inda ya ƙi goyon bayan sauran

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abeokuta, jihar Ogun – Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya musanta ikirarin cewa ya gana da Shugaba Bola Tinubu. Shugaba Tinubu da Obasanjo alaƙa ta yi tsami a tsakaninsu.

Obasanjo ya fito ƙarara ya goyi bayan Peter Obi (Labour Party, LP) a lokacin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, kuma ya riƙa sukar jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Bayyana Shugaban Kasan Najeriya Da a Mulkinsa Aka Samu Bunkasar Tattalin Arziki

Obasanjo ya yi magana kan gana wa da Tinubu
Obasanjo ya karyata batun sanya labule da Shugaba Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ban hadu da Tinubu ba: Obasanjo

An sanya wani faifan bidiyo a dandalin sada zumunta na TikTok mai dauke da sunan “@asiwajuwoldwidef”, inda aka yi iƙirarin cewa Tinubu da Obasanjo sun hadu ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba a bikin cika shekaru 80 na Alake na Egbaland, Oba Adedotun Gbadebo.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Kehinde Akinyemi, ya fitar a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba, Obasanjo ya fusata akan bidiyon ƙaryar da aka yaɗa, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Jaridar Premium Times ta ƙara da cewa a halin yanzu tsohon shugaban na Najeriya yana ƙasar Afirka ta Kudu domin binne Yarima Mangosuthu Buthelezi.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Domin bayyana yadda abubuwan da ke cikin bidiyon suke, ya faru ne lokacin ziyarar da Tinubu ya kai gidansa a shekarar (2022)."

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala Ta Ɓullo Wa Shugaba Tinubu Kan Naɗa Gwamnan Babban Banki CBN

"Ya haɗu da tsohon shugaban ƙasar yana buga wasan gargajiyan da ya fi so (ayo) sai ya fara wasa, cikin raha yana gaya wa tsohon shugaban kasar cewa, ya kaɗu matuka da ya gan shi yana wasan ‘ayo’ a wannan lokacin."

Obasanjo ya bayyana cewa ko sau ɗaya bai ga Tinubu ba a 2023.

El-Rufai Ya Yabi Obasanjo

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Kaduna ya yaba wa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, kan tsarin da ya ɗora ƙasar nan a kai.

El-Rufai ya bayyana lokacin wa'adin mulkin Obasanjo na biyu a matsayin wanda tattalin arziƙin ƙasar nan ya ƙara bunƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng