Kotun Ta Tsare Wasu Matasa 3 Kan Zargin Hayaniya Kusa Da Gidan Ministan Abuja, Wike
- Jami'an tsaro sun cafke wasu matasa a kusa da gidan Nyesom Wike kan zargin tayar da hankali da hayaniya
- Matasan da suka hada da Nasiru Abdullahi da Usman Jibrin da kuma Aliyu Adamu an kama su kan hayaniya da ya addabi mutane
- Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Godwin Gabriel ya fadawa kotu cewa an gargadi matasan da farko amma sun ki ji
FCT, Abuja - An cafke matasa uku tare da gurfanar da su a gaban kotu kan zargin hayanisa da damun jama'a.
An gurfanar da matasan ne a gaban kotun da ke Lugbe a birnin Tarayya, Abuja saboda tashin hankali da su ka jawo.
Meye dalilin tsare matasan kusa da gidan Wike?
Legit ta tattaro cewa wadanda aka kaman sun hada da Nasiru Abdullahi mai shekaru 18 sai Usman Jibrin, 17 da kuma Aliyu Adamu, 18 dukkansu sun amince da laifukansu.
“Rabona Da Wanka Shekara 1”: Yar Najeriya Da Ke Jin Bakin Muryoyi Ta Koka a Bidiyo, Tana Neman Agaji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar cewa an kama matsana ne kusa da gidan ministan Abuja, Nyesom Wike wanda jami'an tsaron ofishin 'yan sanda na Asokoro su ka damkesu.
Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Godwin Gabriel ya fadawa kotu cewar kafin kama matasan an yi musu kashedi amma ba su ji ba.
Meye hukuncin kotu kan matasan da suka dami Wike?
Ya ce an yi bincike sosai kan matasan don sanin dalilinsu na yin hayaniya a wannan kewayen.
Amma ba su bayar da wata hujja gamsasshiya ba na hayaniya a wannan wuri da ke da tsaro.
Alkalin kotun, Mallam Aliyu Kagarko ya umarci ci gaba da tsare su a ofishin 'yan sanda har sai iyayensu sun zo kafin a ba da belinsu.
Ya kuma dage ci gaba da sauraran karar har sai ranar Juma'a 13 ga watan Oktoba, cewar The Guardian.
Wike ya rusa shahararriyar Kasuwa a Abuja
A wani labarin, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ba da umarnin rusa wata shahararriyar Kasuwa a birnin Tarayya, Abuja.
Hukumar FCTA ta rusa kasuwar kilishi da ke birnin a ranar Litinin 18 ga watan Satumbar da mu ke ciki.
Tun bayan hawa kujerar mukamin minista, Wike ke rushe-rushe da jama'a ke ganin bai dace ba wanda su ke ganin hakan asara ne.
Asali: Legit.ng