'Yan siyasa 15 na jihar Kuros Riba na neman kujerar Minista a Majalisar Buhari
A yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kudirci kafa sabuwar majalisar gwamnatin sa a wa'adi na biyu wajen nadin mukaman Ministoci, akwai 'yan siyasa 15 na jihar Kuros Riba da ke hankoron kujerar da za a kebance ga jihar.
Domin neman kasancewa babban jagora na jam'iyya ma ci, kimanin 'yan siyasa 15 na jihar Kuros Riba sun bayyana sha'awar su ta samun nadin mukamin kujerar Minista da gwamnatin shugaban kasa Buhari za ta kebance ga jihar.
Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, masu hankoron kujerar sun kasance jiga-jigan 'yan siyasa na jam'iyyar APC da suka sha mugunyar kaye a hannun 'yan takara na jam'iyyar adawa ta PDP yayin zaben kujejar gwamna, 'yan majalisun tarayya da kuma na jiha.
Rahotanni sun bayyana cewa, mafiya masu hankoron samun nadin mukamin kujerar Minista ta jihar Kuros Riba na ci gaba da fafutikar samun shiga da neman kusanci gami da fadanci ga shugaban kasa Buhari da kuma shugabannin jam'iyyar APC na kasa da kuma yankunan su.
Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, da yawa daga cikin masu hankoron madafar ikon na neman dinke baraka da kuma warware sabani da adawar siyasa da ke tsakanin su da shugabancin jam'iyyar APC na jihar.
KARANTA KUMA: Watan Azumi: Kayan masarufi sun tashi a jihar Legas
Sai dai daya daga cikin jagororin kungiyar yakin neman zaben kujerar shugaban kasa reshen jihar Kuros Riba, Cif Utum Eteng, yayin tsokaci a kan wannan lamari inda ya nemi shugaban kasa Buhari da ya ramawa kura aniyyar ta wajen watsi da duk wadanda suka kawo masa tangarda ta faduwar jam'iyyar APC a jihar yayin babban zaben kasa.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng