An Yi Wa Matashin Mai A-Daidaita-Sahun Da Ya Dawo Da N15m Tayin Yan Mata 4 Da Zai Aura

An Yi Wa Matashin Mai A-Daidaita-Sahun Da Ya Dawo Da N15m Tayin Yan Mata 4 Da Zai Aura

  • Za a karrama matashin nan Auwalu Salisu ɗan shekara 22 da haihuwa, da ƴan mata huɗu saboda gaskiyarsa da nagartarsa
  • Salisu ya zama abin magana ne bayan ya mayarwa ɗan ƙasar Chadi, N15m da ya manta da su a babur ɗinsa a jihar Kano
  • Ƙungiyar haɗa aure wacce aka fi sani da Mai Dalilin Aure, ta ce Salisu ya cancanci a karrama shi da ƴan mata 4

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar KanoAuwalu Salisu, direban a-daidaita-sahun da ya mayarwa ɗan ƙasar Chadi naira miliyan 15, an yi masa tayin ƴan mata huɗu da zai aura.

Ƙungiyar haɗa aure ta Kano wacce aka fi sani da Mai Dalilin Aure, ta ce Salisu zai zaɓi ƴan mata huɗu daga cikin 10 da za a ba shi, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Tsammani Ya Nemi Yan Najeriya Su Yafe Wa Tinubu Kan Laifin Safarar Kwayoyi? Gaskiya Ta Bayyana

Auwalu Salisu ya samu kyautar ƴan mata 4
An yi wa Auwalu Salisu tayin ƴan mata huɗu da zai aura Hoto: @journalistkc
Asali: Twitter

Idan ba a manta ba dai Auwalu Salisu mai shekara 22 a duniya ya zama abin magana ne bayan ya tsinci N15m ciki har da wasu kuɗin CFA, sannan ya nemi mamallakinsu ɗan ƙasar Chadi ya mayar masa da kuɗin.

Tun daga wancan lokaci matashin ya samu yabo sosai daga jami’an gwamnati da kungiyoyi da daidaikun jama’a tare da samun kyaututtuka da dama da suka hada da wani sabon keken a-daidaita-sahu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai a yayin da kungiyar ta bi sahun masu yi masa kyaututtuka, ta yi masa alƙawarin ƴan mata huɗu da zai aura waɗanda za a zaɓo a cikin ƴan mata 10.

Me yasa ƙungiyar ke son karrama Auwalu da ƴan mata 4?

Shugaban kungiyar, Alhaji Mukhtar Inuwa Yakasai, wanda ya bayyana hakan ya ce amincin Salisu, gaskiya da rikon amanarsa ne suka sanya ya cancanci wannan karramawar.

Kara karanta wannan

Karshen Yan Bindiga Ya Zo: Jihar Arewa Ta Dauki Wani Muhimmin Mataki Domin Murkushe Yan Bindiga

Da yake magana a gidan rediyon Freedom da ke Kano, Yakasai ya ce ƴaƴansa mata biyu na cikin waɗanda Salisu zai zaɓa a cikinsu.

A kalamansa:

"Yaron ya nuna kyawawan halayen Manzonmu Annabi Muhammad (SAW). Tabbas shi ɗin mai gaskiya ne. Shiyasa muka yanke shawarar karrama shi da waɗannan kyaututtukan."
"Akwai ƴan mata 10 da zai zabi huɗu daga cikinsu. Biyu daga cikinsu ƴaƴana ne."

Auwalu Salisu Ya Samu Kyaututtuka

A baya rahoto ya zo cewa matashin mai a-daidaita-sahun da ya mayar N15m da ya tsinta a babur ɗinsa ya samu kyaututtuka saboda gaskiyarsa.

Auwalu Salisu mai shekara 22 a duniya ya samu kyautar sabon babur mai ƙafa uku wnada zai riƙa tuƙawa yana neman na abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel