Gwamna Abba Kabir Ya Sha Alwashin Dawo Da Nasararsa Da Kotu Ta Kwace

Gwamna Abba Kabir Ya Sha Alwashin Dawo Da Nasararsa Da Kotu Ta Kwace

  • Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi magana bayan rashin nasarar da ya samu a kotun zaɓen gwamnan jihar
  • A ranar Laraba, 20 ga watan Satumba ne dai kotun zaɓen gwamnan jihar ta ƙwace nasarar da ya samu a zaɓe inda ta tabbatar da ɗan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen
  • Gwamnan ya yi nuni da cewa hukuncin da alƙalan suka yanke cike yake da kura-kurai, inda ya umarci lauyoyinsa da su ɗaukaka ƙara

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya buƙaci al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu sannan ya sha alwashin bin hanyar da doka ta tanada wajen dawo da nasararsa da aka ƙwace.

A jiya Laraba, 20 ga watan Satumba ne dai kotun sauraron ƙarrakin zaɓen gwamnan jihar ta tsige gwamna Yusuf, tare da ba da umarnin a ba wa Nasir Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC takardar shaidar cin zabe.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tsige Ɗan Majalisar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar 'Yan Takarar APC 2 a Jihar Arewa

Gwamna Abba ya magantu kan hukuncin kotu
Gwamna Abba Kabir Yusuf zai daukaka kara kan hukuncin kotu Hoto: Abba Kabir Yusuf, Journalist KC
Asali: Facebook

Da yake jawabi ga manema labarai ƴan mintoci kaɗan kafin tsakar dare, gwamna Yusuf ya ce an tafka kurakurai a yanke hukuncin, kuma yana da ƙwarin gwiwar cewa za a gyara waɗannan kura-kurai a kotun daukaka ƙara, cewar rahoton Daily Trust.

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bayan kusan watanni shida ana shari’a a kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamna, yau Laraba 20 ga watan Satumba, 2023 alƙalan kotun a hikima irin ta su sun yanke hukuncinsu."
"Kamar yadda mutane ne su hukuncinsu ba lallai ya zama daidai ba, akwai kurakurai da rashin amfani da doka kamar yadda lauyoyinmu suka nuna. shi ya sa tsarin mulkin mu ya tanadi wasu matakai domin cigaba da shari'a kamar irin su kotun daukaka ƙara da kotun ƙoli."

Wane mataki na gaba gwamna Abba zai ɗauka?

Gwamnan ya yi nuni da cewa tuni ya umarci lauyoyinsa da su ɗaukaka ƙara kan wannan hukuncin da kotun ta yanke, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Manyan Hadiman Gwamna da Wasu Jiga-Jigai Sun Ƙara Yi Wa PDP Babban Lahani, Sun Koma APC

"Mun riga da mun umurci lauyoyinmu da su daukaka ƙara kan wannan hukunci da wuri-wuri domin tabbatar da cewa an yi adalci." A cewarsa.

Gwamna Abba ya yi kira ga al’ummar Kano da su kwantar da hankula su kuma kasance masu bin doka da oda yayin da aka umarci jami’an tsaro da su tabbatar sun kare rayuka da dukiyoyin al'umma a faɗin jihar.

Gwamnan ya ƙara da cewa:

"Wannan gwamnati za ta cigaba da ƙoƙarin yin aiki domin cigaban jihar mu bisa alƙawuran da muka ɗauka, yayin neman ƙuri’un ku. Muna so mu tabbatar muku da cewa hakan ba zai sa mu karaya ko gwiwoyinmu su yi sanyi ba, domin wannan koma baya ne na wucin gadi ga jihar mu wanda za mu yi nasara da yardar Allah SWT."

Kwankwaso Ya Magantu Kan Hukuncin Kotun Kotu

A wani labarin kuma, tsohon kwamishinan raya karkara na jihar Kano, Dr. Iliyasi Musa Kwankwaso ya yi martani kan hukuncin da kotun zaɓen gwamnan jihar Kano ta yanke na tsige gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Maida Martani Mai Jan Hankali Kan Hukuncin Kotu Na Sahihancin Zaɓen Gwamna

Kwankwaso ya shawarci gwamnan da ya karɓi hukuncin kotun da kyakkyawar zuciya sannan ya buƙace shi da ya haƙura da ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ta yanke.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng