Kotu Ta Ba Da Belin Matasa 'Yan Luwadi 69 Da Aka Kama Su Na Auren Jinsi A Delta
- Babbar kotu a jihar Delta ta ba da belin matasa 69 da ake zarginsu da auren jinsi a karamar hukumar Uvwie da ke jihar
- Jami’an ‘yan sanda sun kama matsan ne a ranar 27 ga watan Agusta yayin da su ke bikin auren jinsi a garin Effurun
- Lauyan wadanda ake zargin, Mista Ochuko Ohimor shi ya bayyana haka a ranar Talata 19 ga watan Satumba ga ‘yan jarida
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Delta – Babbar kotun da ke zamanta a Effurun da ke karamar hukumar Uvwie a jihar Delta ta ba da belin wadanda ake zargi da auren jinsi.
Matasan da aka kama su 69 a jihar su na bikin daura aure sun samu beli a jiya Talata kamar yadda Daily Trust ta tattaro.
Yaushe aka kama 'yan luwadin a Delta?
Jami’an tsaro sun kama matasan ne a ranar 27 ga watan Agusta yayin da su ke bikin auren jinsi da kungiyar su ta shirya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan wadanda ake zargin, Mista Ochuko Ohimor shi ya tabbatar da haka a jiya Talata 19 ga watan Satumba da yamma.
CNN ta tattaro lauyan na cewa:
“Wadanda ake zargin an ba da belinsu a kan kudi har Naira dubu 500 da kuma shaidu guda biyu.
“Wadanda za su tsaya musu dole su kasance mazauna Effurun yankin da aka kama matasan a watan jiya.
“Dole kuma wadanda ake zargin su rinka zuwa kotun da ke Effurun don saka hannu a karshen ko wane wata.”
Yadda aka kama 'yan luwadin a Delta
Idan ba a manta ba an kama su ne yayin da su ke auren jinsi inda 'yan sanda su ka tasa keyarsu zuwa ofishin 'yan sanda na Ekpan.
Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Wale Abass yayin tasa keyar tasu ya yi alkawarin tura su kotu don fuskantar hukunci.
Jami’an tsaro sun kama matasa 'yan luwadi 69 a Delta
A wani labarin, jami’an tsaro sun kai farmaki tare da kama wasu matasa yayin da su ke bikin auren jinsi a jihar Delta.
Matasan an kama su a ranar 27 ga watan Agusta a garin Effurun da ke karamar hukumar Uvwie a jihar.
Hakan ya jawo cece-kuce inda wasu ke ganin an tauye musu hakki na ‘yancin da su ke da shi a matsayin sun a ‘yan kasa.
Asali: Legit.ng