Basaja: Mata 3 sun gano cewa suna soyayya da saurayi 1 a Twitter

Basaja: Mata 3 sun gano cewa suna soyayya da saurayi 1 a Twitter

- Wasu yan mata uku sun bayyana cewa suna soyayya da saurayi daya da duk suka hadu da shi a shafin Twitter

- Shafin Twitter mai suna @KevinEmmilie4 ta wallafa hotunanta da saurayinta, sannan wasu mata biyu suka wallafa nasu hotunan don tabbatar da cewar mutum dayua suke soyayya da shi

- Mabiya kafar sadarwar sun yi sharhi cike da mamakin abunda idonsu ya gane masu

An fallasa wani mutumi da ya hadu da kuma fara soyayya da mata uku a shafin Twitter bayan daya daga cikin matan ta yi jinjina gare shi a dandalin sada zumunta.

Lamarin ya fara ne lokacin da @KevinEmmilie4 ta wallafa hotunanta da na saurayinta sannan ta rubuta:

“A Twitter muka hadu.”

KU KARANTA KUMA: Sanusi II ya yi kira ga mutanen Kano su tsaya a kan koyarwar Shehu Danfodio

Da take martani ga lamarin, wata budurwa mai suna @sharon_kiwanuka a Twitter ta ce itama ta hadu da matashin a Twitter.

Ba da jimawa ba, sai budurwa ta uku a hoton ta fito da nata hujjar don nuna cewa ita ma ta hadu da mutumin a Twitter.

KU KARANTA KUMA: Ba za a iya jan ra'ayinmu don tabbatar da nadin da aka yi wa tsoffin hafsoshin tsaro ba, Majalisa

Tuni mabiya shafin @sharon_kiwanuka suka yi tururuwan sharhi masu ban dariya.

Basaja: Mata 3 sun gano cewa suna soyayya da saurayi 1 a Twitter
Basaja: Mata 3 sun gano cewa suna soyayya da saurayi 1 a Twitter Hoto: @KevinEmmilie4, @sharon_kiwanuka, @HerAcholiness
Asali: UGC

@Obong_Ekpe ya rubuta:

"Amma ga dukkan alamu yana farin ciki sannan kuma kuna farin ciki das hi, don haka ban wani matsala ba a nan.”

@gezbalo ya yi martani:

"Ina bukatar wasu bayanai kan wannan gogan.”

@LaditAbari ya yi martani:

"Ina ganin wannan gayen yana neman abokiyar rayuwarsa ne. Shakka babu zai angwance idan ya samu daya.”

A wani labari na daban, wani mutum a Kaduna ya sa jama’a yamutsa gashin baki a shafin soshiyal midiya bayan ya kwato N5,000 da ya aikewa budurwa amma taki zuwa dakinsa kamar yadda suka yi yarjejeniya.

Mutumin ya kai lamarin gaban kotun majistare lokacin da budurwar taki zuwa dakin nasa sannan tayi ta basa uzuri mara kan gado, sai kotun ta umurci bankin budurwar da ya mayar masa da N5,000 dinsa.

Bankin yayi kamar yadda kotun ta umurta sannan aka mayarwa da mutumin N5,000 dinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel