Jigon APC Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Lakadawa Kwamishina Duka a Ondo

Jigon APC Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Lakadawa Kwamishina Duka a Ondo

  • Jigon APC a jihar Ondo wanda ya lakadawa kwamishina duka ya bayyana dalilinsa na yin hakan
  • Olumide.Awolumate ya bayyana cewa kwamishiniyar ce da ɗanta suka fara takalaraa bayan sun samu saɓani
  • Ya bayyana cewa sun haɗu sun yi masa taron dangi suna dukansa wanda hakan ya sanya dole ya kare kansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo - Wani jigon APC a jihar Ondo, Olumide Awolumate, a ranar Talata, ya bayyana dalilin da ya sa fada ya barke tsakaninsa da kwamishiniyar harkokin mata da cigaban jama’a ta jihar, Misis Juliana Osadahun a Arigidi Akoko, Akoko ta Arewa.

A ranar Lahadi ne Awolumate da Osadahun suka ba hammata iska a wajen shirin raba kayan tallafi ga al’ummar ƙaramar hukumar, cewar rahoton Punch.

Shugaban APC ya magantu kan dukan kwamishina
Shugaban ya bayyana dalilin yi wa kwamishiniyar duka Hoto: Punchng.com
Asali: UGC

Kwamishiniyar ta samu rauni a yayin hatsaniyar, wanda sakamakon haka ne jam'iyyar APC reshen jihar ta dakatar da shugaban gundumar bisa zargin rashin ɗa'a.

Kara karanta wannan

Manyan Hadiman Gwamna da Wasu Jiga-Jigai Sun Ƙara Yi Wa PDP Babban Lahani, Sun Koma APC

Ya bayyana yadda lamarin ya auku

Da yake magana game da abin da ya auku a tsakaninsu, Awolumate ya yi iƙirarin cewa kwamishinan da ɗanta tare da rakiyar wani ɗan sanda da wani mutum ne suka zo gidansa domin kama shi, bai hana a kama shi ba, amma sai ɗan kwamishiniyar ya rufe shi da duka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa a yayin dukan da ya yi masa ya kuma yayyaga masa kaya, wanda hakan ne ya sanya dole ya kare kansa, rahoton The Nation ya tabbatar.

Ya bayyana cewa rigimar ta su ta samo asali bayan an je wajen taro kan yadda za a raba kayan tallafin, inda ya yi ƙorafin na yankinsa ba a ba shi su ba.

Ya ce hakan ya jawo sa'insa a wajen taron inda daga ƙarshe aka umarce shi da ya fice daga wajen taron. Ya ƙara da cewa yana gida kawai yana buga wasan Ludo sai kwamishiniyar da ɗanta da wani ɗan sanda suka yi masa dirar mikiya.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Na Kusa da Atiku Abubakar Ya Tona Asirin Gwamnatin Shugaba Tinubu Kan Abu 1 Tal

A cewarsa, da isa gidansa, ɗan kwamishiniyar kawai sai ya rufe shi da duka, inda ya ce dole ya kare kansa a gaban matarsa da ƴaƴansa.

"Na tashi ina mayar da martani. Muna cikin faɗa kawai sai kwamishiniyar ta taho suka yi min taron dangi ita da ɗanta. Ta fara dukana tana yaga min kaya. Ta dauki kujera ta jefo min ita, nima na rama, ta hanyar jefa mata kujerar." A cewarsa.

Kakakin Majalisa Ya Musanta Batun Tsige Mataimakin Gwamna

A wani labarin kuma, Majalisar dokokin jihar Ondo ta yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa tana shirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Honorabul Lucky Aiyedatiwa.

Rahotanni sun yi nuni.cewa an yi ta cece-kuce da yaɗa jita-jita a ciki da wajen jihar cewa nan ba da jimawa ba majalisar za ta fara aikin tsige shi daga kujerar mataimakin gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel