Kwamishina Ta Sha Dukan Tsiya A Wurin Rabon Kayan Tallafi A Jihar Ondo

Kwamishina Ta Sha Dukan Tsiya A Wurin Rabon Kayan Tallafi A Jihar Ondo

  • Kwamishinar harkokin mata a jihar Ondo ta sha tsinannen duka yayin raba kayan tallafin rage radadi a jihar
  • Kwamishinar mai suna Olubunmi Osadahun ta gamu da tsautsayin ne a yankin Arigidi Akoko na Jihar
  • Wani fusataccen matashi da aka fi sani da 'Cuba' wanda shugaban jam'iyyar APC ne a yankin ya zargi matar da nuna wariya a rabon

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo - Wata kwamishina a jihar Ondo ta sha dukan tsiya bayan an zargeta da nuna wariya wurin raba kayan tallafi.

Kwamishinar wacce ta ke shugabantar ma'aikatar Harkokin Mata a jihar mai suna Olubunmi Osadahun ta gamu da tsautsayin ne a yankin Arigidi Akoko na Jihar.

Kwamishina ta sha dukan tsiya a jihar Ondo
Kwamishina Ta Sha Da Kyar Yayin Da Ta Gamu Da Fushin Matasa. Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi.
Asali: Facebook

Meye dalilin dukan kwamishinar a Ondo?

Lamarin ya faru ne a karshen mako, inda ake zargin mambobin jam’iyyar APC a yankin da yin dukan, bayan sun yi zargin ana nuna wariya a rabon, TheCable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Bayan Lakaɗa Wa Kwamishinar Mata Duka a Wurin Rabon Tallafi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani faifan bidiyo, an gano wani fusataccen matashi mai suna Awolumate Olumide wanda shugaban jam'iyyar APC ne a yankin Akoko ya na cin zarafin matar.

Olumide wanda aka fi sani da ‘Cuba’ ya yi wa kwamishinar dukan tsiya kan zargin ta na son yin almundahana da kayan rabon tallafin.

Wane abu aka yi amfani da shi wurin dukan kwamishinar?

Har ila yau, 'Cuba' ya yi amfani da kujerar zama wurin dukanta a kayi, lamarin da ya yi sanadiyar kumbura mata kai suntum.

Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa rashin fahimtar ta fara ne lokacin da wasu manyan APC suka yi zargin ba a gudanar da harkar rabon a fili.

Hakan ya saka mutanen wurin rashin gamsuwa da rabon da har ta kai ga Olumide daukar wannan mataki, cewar Tribune.

Olumide kamar yadda rahotanni su ka tabbatar ya zargi kwamishinar da mai da shi saniyar ware a wurin rabon kayan tallafin na gwamnatin jiha.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Ɗalibar Jami'ar Tarayya Ta Mutu a Hanyar Zuwa Kasuwa

Kakakin rundunar 'yan Sanda a jihar, Funmilayo Odunlami ta ce har yanzu ba su samu rahoto kan wannan lamari ba.

Gwamna Akeredolu Na Ondo Ya Sallami Hadiman Mataimakinsa

A wani labarin, Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya kori dukkan hadiman mataimakinsa, Lucky Ayedatiwa.

Sakataren yada labaran gwamnan, Richard Olatunde shi ya bayyana haka a ranar Talata 12 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel