Akwai Hasashen Farashin Iskar Gas Na Girki Zai Tashi Nan A Zuwa Watan Disamba A Najeriya

Akwai Hasashen Farashin Iskar Gas Na Girki Zai Tashi Nan A Zuwa Watan Disamba A Najeriya

  • Dillalan iskar gas a Najeriya su ma ba za a bar su a baya ba inda su ka yi hasashen farashin zai tashi a watan Disamba
  • Kungiyar ta dillalan gas din ta sanar da cewa an samu karin farashin ko wani tan ‘yar bazata saboda tashin Dala
  • Shugaban kungiyar, Olatunbosun Oladapo shi ya bayyana haka inda ya ce idan Gwamnatin Tarayya ba ta shiga lamarin ba akwai matsala

FCT, Abuja – Yayin da ‘yan Najeriya ke cikin mawuyacin hali, akwai hasashen cewa gas na girki zai a kara kudi sosai.

Ana hasashen cewa tukunyar gas mai nauyin kilo 12 za ta iya kai wa Naira dubu 18 zuwa watan Disamba, Legit ta tattaro.

Farashin iskar gas na iya karuwa zuwa watan Disamba
Ana Hasashen Farashin Iskar Gas Ma Za Ta Yi Tashin Gwauron Zabi. Hoto: xavier-arnau.
Asali: Facebook

Meye ake hasashe kan farashin gas?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar dillalan iskar gas a Najeriya (NALPGM), Olatunbosun Oladapo ya fitar.

Kara karanta wannan

Ana Wata Ga Wata, Ana Iya Fuskantar Karin Farashin Mai A Najeriya Saboda Dalilai Biyu, Bayanai Sun Fito

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Pladapo ya ce an samu karin Naira miliyan 9 zuwa 14 a ko wane tan 20 wanda hakan ya zo a bazata.

Ya yi gargadin cewa idan Gwamnatin Tarayya ba ta shiga lamarin ba, karin zai iya kai Naira miliyan 18 a kowa ne tan 20 zuwa watan Disamba.

Wannan shi ya ke nuna cewa farashin gasna girki mai nauyin kilo 12 na iya kai wa Naira dubu 18.

Ya ce:

“Akwai hasashen karin kudin gas a yanzu haka, ina tsoron idan Gwamnatin Tarayya ba ta dauki mataki ba, farashin zai kai Naira miliyan 18 a ko wane tan 20.
“Wannan shi ke nuna cewa farashin silindar gas mai nauyin kilogram 12 za ta kai Naira dubu 18 zuwa watan Disamba.”

Meye Oladapo ke cewa kan farashin gas?

Ya kara da cewa wasu na boye gas din inda su ka fake da tashin Dala don kara farashin iskar gas ga ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo: Shinkafa ta sauka a Arewa, buhun masara N20,000 a wata jiha

Idan har hasashen Oladapo ya zama gaskiya, farashin gas mai nauyin kilo 12 zai karu da kaso 96 idan aka kwatanta na Naira dubu 9 a watan Yuli.

Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS ta bayyana cewa a watan Yuli ana siyar da gas mai nauyin kilo 5 a kan Naira dubu 4 ne kacal.

An Samu Sauki Yayin da Farashin Gas Ya Ragu a Najeriya

A wani labarin, Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS ta bayyana cewa farashin iskar gas na girki mai nauyin kilo 5 da 12 ya ragu a watan Mayun 2023.

NBS ta bayyana hakan ne a cikin wani rahotonta na farashi da ta fitar a shafinta na yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.