Gwamnan Kwara Ya Yabawa Tinubu Kan Nada Jamila Bio a Matsayin Ministar Matasa a Najeriya
- Gwamnan jihar Kwara ya bayyana jin dadinsa ga yadda aka nada sabuwar ministar matasa daga jiharsa
- Ya ce ya gamsu da kwarewa da kuma dacewar ba ta wannan mukami mai tasiri da kokarin sauya goben matasa
- Jamila Bio Ibrahim ta taba aiki da gwamnan jihar Kwara, lamarin da ke nuna akwai alaka mai kyau a tsakani
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kwara - Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa ba jihar karin mukamin minista.
Gwamnan na kallon wannan matakin na Tinubu a matsayin wani kyakkyawan mataki na aminci da yarda da jihar saboda biyayyar ’yan Kwara ga jam’iyyar APC mai mulki, rahoton The Nation.
AbdulRazaq ya mika sakon taya murna ga Jamila Bio Ibrahim, tsohuwar babbar mataimakiyarsa ta musamman kan harkokin SDG bisa samun mukamin na ministar matasa.
Mun gamsu da kwarewarta, gwamnan Kwara
Gwamnan ya kara da cewa nadin Jamila ya gamsar da jama'a kan tsarin ci gaban matasa na gwamnan Tinubu na alkawarta karfafawa matasa da damawa da su a mulkin kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tun farko, Tinubu ya sha bayyana cewa, zai yi aiki tare da matasa don ciyar da kasar nan gaba.
Wata sanarwar da aka fitar daga gidan gwamnan jihar ta ce:
“Muna daukar wannan karin nadin a matsayin babban abin alfahari ga jiharmu, musamman duba da matsayin da martabar jam’iyyarmu da na matasa da mata.
"Ba ta karfi da kuma kyakkyawar hanyar sadarwa a tsakaninta matasa, mun yi imanin cewa ta dace da wannan mukamin.
“Gwamnan na yi wa sabuwar minista fatan alheri a sabon aikin da aka ba ta, inda ya bukace ta da ta kasance babbar jakadiyar jihar Kwara APC, da kuma matasa da za ta jagoranta a kasar a yanzu, tare da neman masu ruwa da tsaki da su mara mata baya."
An nada sabbin ministoci
Shugaba Bola Tinubu ya nada sabbin ministoci guda biyu da za sy kula da ma’aikatar matasa, kamar yadda rahoton Channels Tv ya bayyana.
A cewar rahoton, Tinubu ya nada Dr. Jamila Bio Ibrahim da Mista Ayodele Olawande a matsayin wadanda za su rike ma'aikatar.
A tun farko, Tinubu ya mika sunayen wasu ministoci, wadanda tuni majalisa ta amince bayan tantance su.
Asali: Legit.ng