Kotun Zaben Gwamnan Jihar Zamfara Za Ta Yanke Hukunci Ranar Litinin

Kotun Zaben Gwamnan Jihar Zamfara Za Ta Yanke Hukunci Ranar Litinin

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Zamfara ta sanya ranar da za ta yanke hukuncinta kan shari'ar Bello Matawalle da gwman DaudaAwal
  • Bello Matawalle yana ƙalubalantar nasarar da gwamna Dauda Lawal ya samu a zaɓen gwamnan jihar da ya gabata
  • Dukkanin jam'iyyun biyu na APC da PDP sun nuna ƙwarin gwiwarsu na samun nasara a gaban kotun

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Zamfara - Kotun sauraren ƙararrakin zaben gwamnan jihar Zamfara da ke zamanta a Sokoto ta sanya ranar Litinin, 18 ga watan Satumban 2023, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci.

Jaridar Vanguard ta ce kotun za ta yanke hukunci ne kan ƙarar da tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya shigar, yana ƙalubalantar sahihancin zaben da ya kawo Dauda Lawal a matsayin gwamnan jihar.

Kotu za ta yanke hukunci kan shari'ar Matawalle da Dauda
Kotun za ta yanke hukuncinta a ranar Litinin Hoto: Dauda Lawal, Bello Matawalle
Asali: Facebook

Matawalle, wanda a yanzu shi ne ƙaramin ministan tsaro, ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ƙwace nasarar da ya samu a zaɓen, saboda rashin shigar da sakamakon wasu mazaɓu, wanda idan aka haɗa za su sanya ya samu nasara da tazara mai yawa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Ganduje, Gwamnonin APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Dira Wata Jiha, Bayanai Sun Fito

Wacce jam'iyya ce za ta yi nasara a kotun?

Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta ce jam'iyyar na da yaƙinin samun nasara a kotun bayan ta kammala gabatar da ƙwararan hujjoji a gaban kotun.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yusuf Idris, mai magana da yawun jam’iyyar a jihar Zamfara, a lokacin da yake zantawa da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi, 17 ga watan Satumba, ta wayar tarho, ya ce jam’iyyar na fatan dawo da nasarar ta da aka sace.

Ya ce wasu ƙadangarun bakin tulu ne gwamnatin da ta gabata suka yi wa Matawalle zagon ƙasa saboda yadda ya fito fili ya yaƙi shirin sauya fasalin naira da goyon bayan da ya nuna ga Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a lokacin.

Da yake na sa jawabin, muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, Mouktar Lugga ya ce jam’iyyar na da kwarin guiwar samun nasara a kotun.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Soke Zaben Dan Majalisar APC, Ta Ba INEC Umarnin Sake Zabe

Lugga ya bayyana cewa jam'iyyar na da yakinin cewa kotun za ta yi gaskiya da adalci, kuma za ta ba jama'a abin da suka zaɓa.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su yi hakuri kada su wuce gona da iri wajen murna domin suna sa ran samun nasara a ranar Litinin.

Kotu Ta Tanadi Hukunci Kan Zaben Gwamnan Sokoto

A wani labarin kuma, Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto ta tanadi hukuncinta kan ƙarar da aka shigar da gwamna Ahmed Aliyu da mataimakinsa Idris Gobir, na jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Kotun wacce mai shari'a Haruna Mshelia, ta bayyana cewa za ta sanarwa da ɓangarorin biyu ranar da za ta sanar da hukuncinta a cikin watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng