Direban A daidaita Sahu Ya Mayar Da N15m Da Fasinjansa Ya Manta Da Su a Kano

Direban A daidaita Sahu Ya Mayar Da N15m Da Fasinjansa Ya Manta Da Su a Kano

  • Wani matashin direban A-daidaita-sahu a birnin Kano ya yi abun a yaba bayan ya mayar da kuɗin da fasinjansa ya manta da su
  • Matashin mai suna Auwalsu Salisu ya mayar da N15m wanda wani mutumin ɗan ƙasar Chadi ya manta da su a babur ɗinsa
  • Mjtumin wanda ya zo Kano sayayya daga ƙasar Chadi ya yi wa Auwalu kyautar N400k sannan ya godewa iyayensa bisa ba shi kyakkyawar tarbiyya

Jihar Kano - Wani direban keke Napep (A daidaita sahu), mai shekara 22 a duniya ya mayar da tsabar kuɗin da fasinjansa ya manta a babur ɗinsa.

Matashin mai suna Auwalu Salisu ya mayar wa fasinjan na sa, wanda ya taso ɗaga ƙasar Chadi domin yin sayayya a Kano, naira miliyan 15 da ya manta da su, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rashin Tausayi: Wani Matashi Ya Zuba Wa Jaririyar Ɗiyarsa Guba Har Ta Mutu a Jihar Kano Kan Abu 1

Direban A-daidaita-sahu ya mayar da kudin da fasinjansa ya manta da su
Direban ya ce ya kosa kudin su bar hannunsa saboda ba na sa ba ne Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Auwalu Salisu ya mayar da kuɗaɗen ne bayan yaji an bayar da cigiyar kuɗin a gidan rediyo.

Kuɗin da aka manta miliyan 15 sun ƙunshi takardun kuɗin CFA na miliyan 10.3 da takardun kuɗin naira na miliyan 2.9, rahoton Aminiya ya tabbatar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matashin bai san da kuɗin ba

Lokacin da ake hira da shi a gidan rediyon Arewa Radio, Auwalu ya bayyana cewa bai san da kuɗin ba sai bayan ya koma gida yana shirin wanke babur ɗinsa.

Yana yin ido huɗu da kuɗin, bai yi wata-wata ba sai kawai ya sanar da iyayensa, inda suka ba shi umarnin ya koma ko zai ga masu kuɗin a inda ya ajiye fasinjojinsa.

Sai dai, ko da ya koma wajen da ya ajiye su bai same su ba, sai ya dawo gida ya ba mahaifiyarsa kuɗin ta ajiye su a kabat ɗinta

Kara karanta wannan

Abun Kunya: Daga Ba Shi Wurin Zama, Malami Ya Ɗirka Wa Matar Abokinsa Ciki

Auwalu ya ce ya yi matuƙar ƙaguwa kuɗin su bar hannunsa, saboda ba na shi bane, sannan baya da niyyar taɓa ko sisi a ciki saboda hakan bai halatta ba.

Mai kuɗin ya yi masa kyauta

Mai kuɗin wanda ya taso daga ƙasar Chadi zuwa Kano domin yin sayayya, ya bayyana cewa har ya cire ran ganin kuɗin lokacin da matashin ya dawo masa da su.

Mutumin cikin kuka ya bayyana cewa bai yi tunanin har yanzu a duniya akwai masu gaskiya irin su Auwalu ba.

Ɗan ƙasar Chadin ya yi godiya ga iyayen Auwalu, bisa kyakkyawar tarbiyyar da suka ba shi, sannan ya ba shi kyautar naira dubu 400.

Dattijon Da Aka Yi Wa Kyautar Kudi Ys Fashe Da Kuka

A wani labarin kuma, wsni dattijo ya zubar da hawaye bayan wani matashi ya yi masa kyautar kuɗi.

Dattijon wanda tsohpn soja ne ya haɗu da matashin ne bayan ya je banki domin jin ba'asi kan kuɗin fanshonsa tun na shekarar 2002.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel