“Tana Yi Mun Barazana Da Rayuwa”: Magidanci Ya Nemi a Raba Aurensa Mai Shekaru 51

“Tana Yi Mun Barazana Da Rayuwa”: Magidanci Ya Nemi a Raba Aurensa Mai Shekaru 51

  • Wani magidanci ya maka matarsa da suka shafe tsawon shekaru 51 a gaban wata kotun gargajiya da ke jihar Oyo
  • Ojo Olaoye ya zargi matarsa Janet Olaoye da tayar masa da hankali tare da yin barazana ga rayuwarsa
  • Da yake rokon kotun ta raba aurensu, Ojo ya ce ya yi ban kwana da zaman lafiya tun daga lokacin da auri matar tasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Oyo - Wani mutum mai suna Ojo Olaoye, ya roki wata kotun gargajiya da ke Oja Oba, Mopa a Ibadan, jihar Oyo da ta raba aurensa mai shekaru 51 da matarsa Janet Olaoye.

Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta rahoto, Ojo ya zargi matar tasa da taurin kai, yawan fada, tashin hankali da yin barazana ga rayuwarsa.

Magidanci ya nemi a raba aurensa da matarsa
“Tana Yi Mun Barazana Da Rayuwa”: Magidanci Ya Nemi a Raba Aurensa Mai Shekaru 51 Hoto: Tribune Online
Asali: UGC

A cikin karar da ya shigar, Ojo ya ce bai san zaman lafiya ba tun bayan da ya auri Janet wacce ya kwace a hannun wani mutum.

Kara karanta wannan

“Kana Da Kyau”: Wata Uwa Ta Roki Kyakkyawan Saurayi Da Ya Taimaka Ya Auri Diyarta

Ban san zaman lafiya ba tunda na auri matata - Magidanci ya koka

Wanda ke karar ya yi bayanin cewa wacce ake kara ta bijire kuma a kodayaushe tana kin bin umurninsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da cewar a kullun cikin fada suke saboda bata biyayya, sai dai gogayya da shi a gida.

A cewarsa, sun samu sabani yan kwanaki da suka gabata kafin ta tattara ta bar gidansa kuma cewa ta nuna masa wuka.

Ojo ya kuma bayyana cewa Janet na da dabi'ar cire masa wando da jansa idan tana fada da shi.

Ya kara da cewar wasu lokutan ta kan ja masa mazakutansa sannan ba za ta saki ba har sai makwata sun zo sun cece shi.

Mai shigar da karar ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ta danne masa tauraronsa da na yaransu ta hanyar tsine masu a kullun.

Kara karanta wannan

Rashin Imani Yayin Da Aka Cafke Matashi Kan Satar Kodar Wani Ba Tare Da Ya Sani Ba, Tuni Ya Siyar Da Ita

Bugu da kari, Ojo ya ce Janet ta kasance uwar gulma mai shiga daga wannan gida zuwa wancan gida tana yana abubuwan da ke faruwa a garinsu da kuma tona sirrin iyalinta.

Ya kuma fada ma kotun cewa ya sa yan sanda sun kama tare da tsare matar tasa a karon karshe da ta je gidansa bayan ta fice daga gidan aurensu.

Ya bayyana cewa Janet ta yi korafi da fada da shi tsawon daren sannan ta hana shi samun bacci don hutawa a wannan daren.

Saboda haka, ya roki kotu da ta hana ta zuwa gidansa don yin fada da shi. Sannan ya nemi a hana ta zuwa cin zarafinsa tare da yi masa barazana.

Sai dai kuma, a nata bangaren, Janet ta karyata duk zarge-zargen da ake mata sannan ta ki yarda a raba aurensu.

Shugabar kotun, Misis S.M Akintayo, ta dage sauraron shari'ar zuwa wani lokaci don matar ta fadi nata bayanin.

Kara karanta wannan

Azarɓaɓin Hadimin Tinubu Ya Jawo An Ji Kunya, Gwamnati Tayi Ƙarya a Ƙasar Waje

Shekaru biyu mijina bai hada gado da ni ba, matar aure ta je kotu

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matar aure ta koka a gaban wata kotun Shari'a da ke Rigasa, jihar Kaduna inda ta nemi a raba aurensu.

Ruqayya ta ce tsawon shekaru biyu mijinta na sunna, Naziru Hamza bai kwanta da ita ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng