Hotunan Shagalin Bikin Wani Mutum Da Ya Auri Mata 7 a Rana Daya Sun Yadu

Hotunan Shagalin Bikin Wani Mutum Da Ya Auri Mata 7 a Rana Daya Sun Yadu

  • Wani mutum mai suna Habib Nsikonnene ya angwance da tsala-tsalan yan mata bakwai a rana daya
  • Habib wanda ya kasance shahararren dan kasuwa ya gwangwaje matan nasa da sabbin motoci a ranar bikinsu
  • Matashin angon ya kuma bayyana aniyarsa na kara wasu matan a nan gaba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani babban dan kasuwa a kasar Uganda, Habib Nsikonnene, ya auri mata bakwai a ranar Lahadi, 10 ga watan Satumba a kasarsu.

Kamar yadda Capital FM Uganda ta rahoto, biyu daga cikin matan nasa sun kasance yan uwa na jini.

Habib ya aure mata bakwai a rana daya
Hotunan Shagalin Bikin Wani Mutum Da Ya Auri Mata 7 a Rana Daya Sun Yadu Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Bayan an daura masu aure, Nsikonnene da matansa bakwai sun jeru a cikin wani abun hawa inda suka karade yankunan Kalagi, Kasana, Nakifuma, kafin su isa gidansu da karfe shida na yamma.

An fara shagalin bikin ne da kade-kade a yayin da ma'auratan suka shiga cikin ayarin motocin da suka yi dafifi a kan titi domin shaida bikin.

Kara karanta wannan

A Kokarin Gyara A Harkar Ilimi, Abba Kabir Ya Dauki Mummunan Mataki Kan Wasu Shugabannin Makarantu 2 A Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu mutane sun kasa yarda cewa hakan gaskiya ne, wasu kuma sun ce wannan ne karo na farko da suka shaida irin wannan biki na tarihi kuma ba sa tunanin cewa a rayuwarsu za su sake ganin wani mutum kamar Habib yana abu makamancin wannan.

Nsikonnene ya auri Mariam, Madinah, Aisha, Zainabu, Fatuma, Rashida, da Musanyusa, wacce aka rahoto cewa ita ce uwargidarsa kuma sun shafe tsawon shekaru bakwai tare.

Ina da burin kara wasu matan a gaba - Ango Habib

Har ila yau, an rahoto cewa Nsikonnene ya siya sabbin motoci inda ya gabatarwa kowannensu a matsayin kyauta, kuma kowacce na dauke da sunanta a jikin motarta.

Da yake jawabi a wajen liyafar bikin, angon ya jinjinawa matan nasa kan zamowa masu biyayya a gare shi.

Ya kuma bayyana cewa yana burin kara auren wasu matan a nan gaba.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnan PDP Ya Saka Tukwicin N100m Kan Makashin DPO, Ya Dakatar Da Basarake Har Sai Baba Ta Gani

Ya ce:

"Matana basa kishi a tsakaninsu. Na gabatar da su ga junansu daban-daban sannan na yanke shawarar aurensu a lokaci daya domin kafa babban iyali mai cike da farin ciki. Har yanzu ni matashi ne kuma a nan gaba, da yardar Allah, ba zan iya cewa wannan ne karshe ba."

Ga hotunan shagalin bikin a kasa:

Yadda juna biyu ya sauya kamannin wata mata, ta koma tamkar ba ita ba

A wani labari na daban, mun ji cewa dandalin soshiyal midiya ya dauki dumi bayan wata mata ta shiga shahararriyar gasar nan ta TikTok.

A cikin bidiyon da ya yadu, ta baje kolin yadda rayuwarta ta kasance a lokacin da take dauke da juna biyu da yadda kamanninta ya koma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng