Mutane Sun Daka Wawa Kan Motoci 3 Dauke Da Shinkafar Da Za A Raba Tallafi A Jihar Kwara
- Yayin da ake cikin halin kunci a Najeriya, wasu mutane sun daka wawa kan abincin tallafi a jihar Kwara
- Mutanen sun yi warwason ne yayin da wasu motoci uku su ka dauko buhunan shinkafa don kai su masauki a jihar
- Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Okasanmi Ajayi ya ce ba su da labarin faruwar lamarin amma zai yi bayani da zarar ya samu
Jihar Kwara - Wasu matata sun afkawa motar da ke dauke da buhunan shinkafa na rabon tallafi a jihar Kwara.
Matasan sun daka wawa a kan wasu motoci uku da ke dauke da shinkafar da za a raba tallafin shugaba Tinubu a wasu yankuna a Jihar.
Matasa sun daka wawa kan kayan tallafi a Kwara
Aminiya ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a yankunan Oja-Oba da Idi-Ape da Isale-Oja da ke kananan hukumomin Ilorin ta Gabas da Ilorin ta Yamma.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton ya bayyana cewa hakan ya faru a ranar Juma'a 8 ga watan Satumba da yammaci kusa da ofishin 'yan sanda.
A cikin wani faifan bidiyo, an gano mutanen na jefo buhunan ga jama'a yayin da su ke dibar kasonsu ba wani shamaki.
Martanin 'yan sanda kan satar kayan tallafi a Kwara
Wata majiya daga yankin ta tabbatar cewa jami'an tsaro sun dawo daga baya inda su ka gudanar da tambayoyi amma ba su kama kowa ba.
Kakakin Rundunar ’yan sanda a jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce har zuwa tattara wannan rahoto ba su samu labarin faruwar hakan ba, BusinessDay ta tattaro.
Sai dai Ajayi ya yi alkawarin cewa da zarar ya samu karin bayani zai sanar da manema labarai.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan biyar ga ko wace jiha a Nijeriya don rage radadin cire tallafin mai.
Matasa sun fasa rumbun abinci na tallafi a Bayelsa
A wani labarin, wasu mazauna garin Yenagoa babban birnin jihar Bayelsa sun kai farmaki a rumbun gwamnati.
Mutanen sun kai farmakin ne a daren ranar Lahadi 27 ga watan Agusta, kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.
Ba a tabbatar ba ko a cikin kayan da aka satan akwai tallafin Shugaba Bola Tinubu da ya yi alkawari.
Asali: Legit.ng