Bayan Shafe Tsawon Shekaru 10 Tana Aikin Kula Da Yara, An Mallakawa Matashiya Gida a Abuja

Bayan Shafe Tsawon Shekaru 10 Tana Aikin Kula Da Yara, An Mallakawa Matashiya Gida a Abuja

  • Wani bidiyon TikTok mai tsuma zuciya ya nuno yanayin wata mai aikin reno lokacin da uwar dakinta ta gwangwajeta da gida a Abuja bayan shekaru 10 tana aiki
  • Mai aikin, wacce ke kula da yaran uwar dakin tata, ta bayyana yadda ta kasance mai gaskiya da himma a kan aikinta
  • Uwar dakin tata ta yanke shawarar saka mata saboda kwazo da jajircewarta ta hanyar bata hadadden gida nata na kanta

Wani bidiyo mai tsuma zuciya da ya yadu a dandalin TikTok, ya nuna lokacin da wata mai aikin reno ta karbi kyautar gida a Abuja daga wacce ta dauketa aiki bayan shekaru goma a aiki.

Mai aikin, wacce ta sadaukar da shekaru goma tana kula da yaran uwar dakinta, ta bayyana yadda ta kasance mai amana da jajircewa a kan aiki.

Kara karanta wannan

“Na Ga Rayuwa Da Ciki”: Bidiyon Sauyawar Wata Mata Kafin Ta Haihu Ya Girgiza Intanet

Uwar daki ta gwangwaje yar aikinta da kyautar gida
Bayan Shafe Tsawon Shekaru 10 Tana Aikin Kula Da Yara, An Mallakawa Matashi Gida a Abuja Hoto: TikTok/@metuo_visuals
Asali: TikTok

Mai aikin reno ta samu kyautar gida daga uwar dakinta bayan shekaru 10

Uwar dakin tata, mai karamci ta nuna godiya kan kwazon aiki da jajircewar mai aikin tata ta hanyar mallaka mata gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ya hasko farin ciki da godiyar mai aikin yayin da ta tsaya kusa da sabon gidanta.

Legit.ng ta lura cewa kafofin watsa labarai da dama ma sun rahoto labarin amma basu iya jin ta bakin mai aikin ba a daidai lokacin kawo rahoton.

Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka kalli bidiyon sun yi godiya ga mai aikin da uwar dakin tata kan halaccin da suka nunawa junansu.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

Hijay cosmeticz ta ce:

"Wannan ya yi kyau sosai."

Aisha O ta rubuta:

Kara karanta wannan

“Kada Ku Kuskura Ku Bar Matayenku Ku Tafi Turai”: Dan Najeriya Da Ke Zaune a UK Ya Gargadi Ma’aurata

"Allah ya albace ki da ahlinki."

MurphyLolo557 ya yi martani:

"Ma shaa Allah, Allah ya albakace ki."

Ayarin motocin matar gwamnan Bauchi sun makale a tabo

A wani labari na daban, mun ji cewa ayarin motocin matar gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Aisha Bala Muhammad, sun makale a cikin ambaliyar ruwa a hanyarsu ta zuwa tafiya.

Wani mai amfani da manhajar X Ainà Dipo @dipoaina1 ya tabbatar da lamarin a wata wallafa da ya yi a shafinsa tare da hotunan.

A cikin rubutun nasa wanda Legit.ng ta gano, ya alakanta halin da matar gwamnan Bauchin ta shiga da irin abun da ya faru da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng