Yar Najeriya Ta Mutu a Jirgin Egypt Air, An Yasar Da Gawarta a Alkahira

Yar Najeriya Ta Mutu a Jirgin Egypt Air, An Yasar Da Gawarta a Alkahira

  • An rahoto cewa wata yar Najeriya ta mutu a cikin shahararren jirgin sama, a hanyarta ta zuwa kasar Birtaniya
  • Yan uwan matashiyar basu samu kowani bayani da ke bayyana musababbin mutuwarta ba amma an ajiye gawarta a Alkahira, babban birnin Masar
  • Jirgin Egypt Air bata yi martani kan wannan al'amari ba kuma bata tuntubi yan uwan marigayiyar kan mutuwarta ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta gamu da ajalinta. Matashiyar matar ta mutu ne a cikin jirgin sama na Egypt Air a hanyarta ta zuwa birnin Landan, kasar Birtaniya, Daily Trust ta rahoto.

Fasinjar Najeriya ta mutu a Egypt air
An yi amfani da hoton don kwatance ne mutanen da ke ciki basu da alaka da rahoton da ake magana a kai Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto
Asali: Getty Images

An rahoto cewa matashiyar wacce ba a bayyana sunayenta ba, ta baro Najeriya zuwa Landan a cikin jirgin Egpyt Air mai lamba MS 876 zuwa Alkahira a ranar Litinin, 4 ga watan Satumba, ta filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagas lokacin da ta mutu a cikin jirgin.

Kara karanta wannan

Kaico: Kawaye sun lakadawa wata mata duka kan wawashe kudi a wurin biki

Wata majiya ta iyalin sun yi martani kan mutuwar matashiyar

Wata majiya ta iyalin wacce ta tabbatar da lamarin, ta ce jirgin ya ajiye gawar a Alkahira, babban birnin kasar Masar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Iyalin sun ce kamfanin jirgin bai sanar da su ba, amma maimakon haka sun samu wani sako daga ofishin karamin ofishin jakadancin da ke birnin Alkahira inda aka sanar da su labarin mutuwarta a cikin jirgin. Don Allah suna bukatar sanin ainihin abin da ya faru da kuma yadda za a dawo da gawar ta Najeriya,” in ji wata majiya ta kusa da dangin.

Daily Trust ta tattaro cewa matashiyar za ta Landan da bizar dalibai sannan ta shiga jirgin Egypt Air wanda zai sada ta da Landan.

Za a sada ta da Landan ta jirgin Egypt Air MS777 a washegarin ranar.

Kara karanta wannan

“Aikin Mijinta Ne”: Hotunan Yadda Ayarin Motocin Matar Gwamnan Bauchi Suka Makale a Tabo

A halin da ake ciki, babu wani martani nan take daga Egypt Air a daidai lokacin kawo rahoton amma wata majiya ta ce jirgin sun ce suna jiran bayanai daga Alkahira kan lamarin.

Tashin Hankali Yayin da Jirgin Sama Ya Gamu da Hatsari Bayan Ya Sauka a Legas

A wani labarin, mun ji cewa wani jirgin saman fasinjoji na kamfanin United Nigeria Airlines ya sauka daga titin tashi da saukar jiragen sama a filin jirgin Murtala Muhammed (NMA) jihar Legas.

Jaridar Daily Trust jirgin ya samu matsalar da ta kai ga sauka daga asalin titinsa na tashi ko sauka, lamarin da ya haifar da firgici da tashin hankali tsakanin Fasinjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng