An Kama Fasinja Kan Satar Kwamfutar Tafi Da Gidanka a Cikin Jirgin Sama a Legas

An Kama Fasinja Kan Satar Kwamfutar Tafi Da Gidanka a Cikin Jirgin Sama a Legas

  • Dubun wani fasinja ta cika yayin da aka kama shi ya saci kwamfutar tafi da gidanka a cikin jirgin sama
  • Lamarin ya faru ne a Legas, yayin da jirgin ke shirin tasowa zuwa Abuja babban birnin tarayya
  • Bincike da aka shafe kusan rabin sa'a ana gudanarwa ne ya taimaka wajen gano kwamfutar a wajen ɓarawon mai suna David

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Legas - An kama wani fasinjan jirgin sama bisa zargin satar kwamfutar tafi-da-gidanka ta wani fasinja.

An kama fasinjan mai suna Ogeneochuko David a cikin wani jirgi na kamfanin Ibom Air mai lamba Q1300 da ya taso daga Legas zuwa Abuja a ranar 26 ga Yuli, 2023.

An ce David ya saci kwamfutar tafi-da-gidankan ne daga jakar wani fasinja da aka aje wajen da ake ajiye kaya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Ali Nuhu Ya Taya Al'ummar Nijar Alhinin Halin Da Suke Ciki

An kama barowon kwamfuta a jirgin sama
An kama wani fasinja kan satar kwamfuta a cikin jirgin sama. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai kwamfutar ne ya gano barawon

Mai kwamfutar bai gamsu da yadda David ke kai kawo a cikin jirgin ba, wanda hakan ya sa ya yanke shawarar duba inda ya ajiye kwamfutar tasa.

Daga nan ne ya fahimci cewa an ɗauke masa kwamfutar, wanda nan take ya sanarwa da ma'aikatan jirgin halin da ake ciki.

An gudanar da bincike da ya ɗauki kusan rabin sa'a, inda daga ƙarseh aka gano kwamfutar a wajen Mista David.

Mai magana da yawun kamfanin na Ibom Air, Aniekan Essienette, wacce ta tabbatar da kama fasinjan, ta ce nan take aka sauke fasinjan kuma aka miƙa shi ga jami'an tsaro na Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN) don gudanar da bincike.

An miƙa barawon kwamfutar ga jami'an 'yan sanda

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Ƙara Samun Fashewa a Najeriya, Mutane Sama da 20 Sun Mutu

Ta ce daga baya kuma an miƙa wanda ake zargin zuwa ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Ta ƙara da cewa, hukumar ‘yan sanda ta tabbatar musu da cewa wanda aka kama ɗan wata babbar ƙungiya ce da ta ƙware wajen sata a cikin jiragen sama.

Ta kuma ce mai kwamfutar ma yau haƙura da tafiyar, inda ya sauka daga jirgin da radin kansa don taimakawa wajen gudanar da bincike kuma ya yi alƙawarin bin diddiƙin lamarin har zuwa karshensa.

Jirgin sojojin saman Najeriya ya yi haɗari a Benue

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan haɗarin da jirgin sojojin saman Najeriya ya yi a Makurdi da ke jihar Benue.

Lamarin ya faru ne ranar Juma'a, 14 ga watan Yuli yayin da jami'an ke gudanar da wani atisaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng