“Idan Kana Son Zama Mai Arziki Ka Zama Mai Kankamo”, Fitaccen Mawaki Akon Ya Ce Ya Fi Kowa Kankamo a Duniya

“Idan Kana Son Zama Mai Arziki Ka Zama Mai Kankamo”, Fitaccen Mawaki Akon Ya Ce Ya Fi Kowa Kankamo a Duniya

  • Shahararren mawakin nan dan kasar Senegal, Akon ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya bayar da shawara mai ban mamaki kan kudi
  • Fitaccen mawakin wanda ya zama bako a wani shiri ya yi bayanin cewa hanyar da mutum zai ci gaba da zama mai arziki shine ya zama mai kankamo
  • Shawarar Akon kan yadda mutum zai ci gaba da zama mai arziki ya zama abun magana a tsakanin jama'a inda suka bayyana ra'ayoyinsu

Shahararren mawakin nan dan kasar Senegal, Akon, ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi kowa kankamo a duniya.

Fitaccen mawakin ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a matsayin bako a wani shiri tare da Logan Paul.

Akon ya ce shine shugaban yan kankamo na duniya
“Idan Kana Son Zama Mai Arziki Ka Zama Mai Kankamo”, Fitaccem Mawaki Akon Ya Ce Ya Fi Kowa Kankamo a Duniya Hoto: @akon, @impaulsiveshow
Asali: Instagram

A yayin shirin, Akon ya bayyana cewa hanya mafi dacewa da mutum zai ci gaba da zama mai arziki shine ya zama mai kankamo.

Kara karanta wannan

Rashin Tarbiyya: Matashi Ya Dannawa Mahaifansa Kwado A Daki Su Na Bacci, Ya Musu Mummunan Sata

A cewar mawakin, ya taba yunkurin mallakar jirgin sama nasa na kansa amma kuma tsawon watanni shida kawai ya yi da shi kafin ya siyar. Ya ci gaba da cewar abun da mutum yake kashewa wajen kula da jirgin ya fi ainahin kudin siyan jirgin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akon ya bayar da shawarar cewa ya fi ace mutum ya siya yan awanni a cikin jirgi sannan ya yi amfani da shi idan ya zama dole kamar idan suna kulla yarjejeniya.

Daga karshe, mawakin ya bayyana cewa yana yawan fada ma mutane da su kashe kudin da suke da shi a yanzu ta yadda zai kai su muddin rayuwansu saboda wannan zai sauya yadda suke kashe kudi.

Kalamansa:

"Idan kana son zama da arziki, ka zama mai kankamo. Na fi kowa kankamo a duniyar nan. Na yi yunkurin mallakar jirgin sama na kaina, wannan abun bai wuce watanni 6 ba, na gaggauta siyar da abun nan. Ka siya yan awanni sannan ka yi amfani da shi idan ya zama dole sannan yawanci ka yi amfani da shi a matsayin hanyar kulla yarjejeniya, ka bari wannan ya zama dabarar samun kudi amma a duk abun da za ka yi, kada ka mallaki jirgin sama. Mallakar jirgin sama daidai yake da kashe dala miliyan biyu, uku a shekara don kula da shi kawai. Ka fi kashe kudi kan kula da shi fiye da siyan ainahin jirgin. Wannan ita ce shawarar da nake ba kowa, kudin da kake da shi a yanzu dole ya kai ka muddin rayuwa, idan ka yi tunani a kan haka, yadda za ka kula da komai zai sha banban."

Kara karanta wannan

Wani Mutum Da Ya Fara Sana’ar Ayaba Da Kasa Da N100k Ya Gina Gida 3, Yana Shirin Fadin Sirrin

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin jama'a yayin da Akon ya ce shine shugaban yan kankamo na duniya

infinitykay_xx:

"Yana da yara kamar 10, don haka ba sabon abu bane ya zama mai kankamo."

ahmad__jay:

“Toh! Wani attajiri mai karimci ya yi magana."

olufisayo_s:

"Babban darasin kudi!!!"

onyinyeeeee:

"Mutumin nan makaranta daya suka je da Obi."

Dan Najeriya da ya fara sana'ar ayaba da kusan N100k ya gina gida na 3

A wani labari na daban, wani hazikin dan Najeriya da ke sana'ar siyar da soyayyen ayaba ya nunawa duniya gidan da yake ginawa.

Mutumin mai suna @adegbengaolusegun ya ce ginin shine gida na uku da ya gina tun bayan da ya fara sana'ar siyar da soyayyen ayaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng