"N778k Duk Wata": Wani Mutum Da Ke Zaune a Turai Ya Saki Bidiyon Gidan Haya Da Ake Biyan N778k

"N778k Duk Wata": Wani Mutum Da Ke Zaune a Turai Ya Saki Bidiyon Gidan Haya Da Ake Biyan N778k

  • Wani mutumi da ke zama a Canada ya nunawa yan TikTok irin gidan da za su iya samu kan N778k duk wata a kasar
  • Mutumin, Benny Tours Canada, ya ce gidan na a New Brunswick, kuma ya baje kolin yadda cikinsa yake
  • Benny ya rigada ya biya kudin gidan kuma tuni ya koma zama a cikinsa tare da iyalinsa, ya kuma ce yana dauke da dakuna biyu da bandaki

Wani mutumi da ke zama a Canada ya zagaya da mutane cikin gida mai dakuna biyu da yake biyan N778k duk wata.

Mutumin mai suna Benny Tours Canada, ya wallafa bidiyon gidan wanda yake a yankin New Brunswick, Canada.

Wani mutum ya baje kolin gidansa a Canada
"N778k Duk Wata": Wani Mutum Da Ke Zaune a Turai Ya Saki Bidiyon Gidan Da Ake Biyan N778k a New Brunswick Hoto: TikTok/@bennytourscanada.
Asali: TikTok

A wannan farashin na N778k duk wata, hakan na nufin masu haya a gidan za su dunga biyan naira miliyan 9.3 duk shekara a matsayin kudin haya.

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Magana, Ya Haska ‘Barnar’ da Gwamnatin Buhari Tayi a Shekaru 8

Benny, wanda tuni ya tare a gidan, ya bayyana cewa bai zo da kayan daki ba domin dai dan haya ne zai siya kayayyakin amfaninsa da kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma ya ce gidan na da wifi, wutar lantarki, ruwa da abun dumama wuri kuma duk wadannan na cikin kudin hayar gidan.

Dakuna biyun na dauke da bandaki da kuma kuma wani dakin yara.

Mabiya shafinsa na TikTok sun nuna sha'awarsu a kan gidan.

Kalli bidiyon a kasa:

Martanin yan TikTok yayin da mutumin da ke zaune a Canada ya baje kolin cikin gidansa

@Dankoky ya ce:

"Don Allah za ka iya magana game da Ontario?"

@afam46 ta yi martani:

"Hanyar da ka bi wajen isarwa mutane da sako ya burge sosai. Allah ya albarkace ka."

Abhiba_xx ta tambaya:

"Don Allah yana zuwa da kayan daki ne?"

Kara karanta wannan

Baturiya Ta Saki Hotuna Yayin da Ta Fallasa Masoyinta Dan Najeriya Wanda Ya Barta Da Ciki a Turai Don Auren Yar Najeriya

@Alex ta tambaya:

"Muna nan tafe kwanan nan, don Allah ta yaya za ka taimaka dangane da hayar gida?"

@Desmond ya tambaya:

"Mutum zai iya biyan kudin hayar wata daya kawai a Canada."

Wani mutum ya shiga tasku bayan ya siya motar hannu, kofar bata buduwa

A wani labari na daban, wani dan Najeriya ya siya wata motar hannu kan kudi N330k don amfanin iyalinsa, amma sai abun ya zama ciwon kai.

Matar mutumin ta garzaya soshiyal midiya don bayyana yadda motar ta dunga kunyata su tun bayan da suka kai ta gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel