Gwamnatin Buhari ta ware miliyoyin kudi domin aikin wutan Mambilla a shekarar 2022

Gwamnatin Buhari ta ware miliyoyin kudi domin aikin wutan Mambilla a shekarar 2022

  • Gwamnatin Tarayya ta sa Naira miliyan 650 na aikin Mambilla a kasafin 2020
  • Haka zalika ana kyautata zaton za a karasa aikin Zungeru hydropower a badin
  • Najeriya ta ware Naira biliyan 1.6 domin a saye motocin fadar Shugaban kasa

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi kasafin Naira miliyan 650 a matsayin kasonta na kwangilar wutar lantarkin Mambilla a shekarar 2022 mai zuwa.

A tsarin yarjejeniyar aikin wutan Mambilla, gwamnatin tarayya da kasar Sin za su yi karo-karo domin ayi wannan aiki da ake lissafi zai ci Dala biliyan 5.

Jaridar Daily Trust tace kasa da Naira biliyan daya gwamnatin tarayya ta ware wa wannan aikin.

Aikin na Mambilla yana cikin muhimman ayyukan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ci burin yi, ganin ta yi alkawarin inganta harkar wuta a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon Jigon APC yace ‘Yan Najeriya su shiryawa bakar wahala bayan ganin kasafin 2022

Najeriya ta ware wa motoci sama da Naira biliyan 1.5

A daidai wannan lokaci kuma, rahoton yace gwamnati ta ware Naira biliyan 1.6 domin a canza motocin da ke cikin fadar shugaban kasa a shekarar badi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadannan makudan kudi za su tafi wajen sayen wasu motoci da gyaran wadanda ake amfani da su.

Buhari
Shugaba Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Kudin da aka ware domin motocin Aso Villa a kasafin shekarar 2022 ya nunka abin da ake sa ran za a kashe wajen aikin Mambila kusan sau biyu da rabi.

A jawabin da Ministar kudi ta kasa, Zainab Ahmed ta yi, tace akwai wasu muhimman ayyuka da gwamnati za ta maida hankali a kansu a shekara mai zuwa.

Daga ciki har da kwangilar Mambila wanda zai ci Naira miliyan 650. Ministar tace an cire kudin da za a ba masanan da suke bada shawarar yadda za ayi aikin.

Kara karanta wannan

Babu maganar wahalar man fetur, kungiyar NUPENG ta fasa tafiya yajin-aiki a yau

Za a batar da kudi wajen samar da hasken wuta

Wani abin farin ciki shi ne kudin da aka ware wa ma’aikatar wuta ya karu. Ana sa rai ma’aikatar ta ci N301b, akasin N204bn da aka yi mata kasafi a shekarar bara.

Ana sa ran a shekarar 2022, a kashe kudi wajen aikin Kashimbilla da tashar samar da wuta ta iska da ke Katsina, sannan aikin Zungeru hydropower zai ci 40bn.

Ana ta gafara sa a Najeriya

Kun ji aikin na Mambilla ya ci sama da Naira biliyan 10 a shekaru shida, amma ba a ga komai a kasa ba. Kwanakin baya aka ji cewa kwangilar ba ta je ko ina ba.

Kamfanin Sunrise Power Transmission Company of Nigeria Ltd ya kawo cikas a aikin samar da wutar lantarkin, bayan ya kai gwamnati kotu yana neman N200bn.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2022: Fadar shugaban kasa za ta kashe N1.6bn wurin siyan sabbin ababen hawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel