Hukuncin Kotu: Rabaran Mbaka Ya Gaya Wa Tinubu Ya Shirya Barin Ofis, Gaskiya Ta Fito

Hukuncin Kotu: Rabaran Mbaka Ya Gaya Wa Tinubu Ya Shirya Barin Ofis, Gaskiya Ta Fito

  • Wasu batutuwa sun bayyana a yanar gizo masu cewa Ejike Camillus Anthony, wanda aka fi sani da Mbaka, ya gaya wa Shugaba Tinubu ya shirya barin ofis
  • Wanda ya sanya bidiyon ya kuma yi iƙirarin cewa Mbaka ya ce gwamnatin Tinubu na dab da zuwa ƙarshe saboda ubangiji baya farin ciki da shi
  • Legit.ng ta yi bincike kan batun inda ta gano cewa maganar da faston ya yi a ranar 18 ga watan Agusta, sauyata aka yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Wata tashar YouTube mai suna, SkyPost TV, ta yi iƙirarin cewa sanannen faston nan ɗan jihar Enugu, Rabaran Ejike Mbaka, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya shirya barin ofis.

Bidiyon wanda aka wallafa a ranar Juma'a, 25 ga watan Agustan 2023, ya nuna Mbaka yana magana kan halin da ƙasa take ciki a cocinsa. Mutane da dama sun kalli bidiyon mai tsawon minti takwas.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Sako Dakataccen Karamar Hukumar Jihar APC da Ta Tsare, Bayanai Sun Fito

Maganar gaskiya kan batun Rabaran Mbaka kan Shugaba Tinubu
Kalaman da Rabaran Mbaka ya yi sauya su aka yi Hoto: Adoration Ministry Enugu Nigeria - AMEN, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

An sauya kalaman Mbaka

A ranar Talata, 5 ga watan Satumba, batun wanda ya samu asali daga tashar YouTube (SkyPost) an sake yaɗa shi a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne ana saura kwana ɗaya kotun zaɓen shugaban ƙasa ta yanke hukuncinta kan ƙarar da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party suka shigar domin ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu.

Wani mai amfani da sunan Odoh Gideon

a Facebook, ya rubuta cewa:

"Ka shirya barin ofis, gwamnatinka na dab da ƙarewa saboda ubangiji baya farin ciki da kai, (Rabaran Mbaka) ya gargaɗi Tinubu a cikin sabon bidiyo

Gaskiyar yadda batun yake

Babu wani sahihin rahoto mai cewa Mbaka ya faɗi abin da aka ƙaƙaba masa.

Legit.ng ta kalli bidiyon da aka yanke, inda ta gano cewa maganar gaskiya ita ce wanda ya sanya bidiyon sauya kalaman Mbaka ya yi.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Shugaban Mulkin Sojin Mali Ya Yi Barazanar Farmakar Abuja Da Cire Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

Kalaman Mbaka na cewa:

"Sama na kallon Shugaba Tinubu. Idan ya miƙa lamarinsa ga ubangiji, ubangiji zai yi amfani da shi wajen ceto ƙasar nan. Idan baya son miƙa lamuransa ga ubangiji, wani mummunan abu wanda ya fi na Jamhuriyar Nijar zai faru a Najeriya. Ban san ta yaya ko yaushe hakan zai faru ba."
"Ƴan Najeriya na kallonka (yana nufin Shugaba Tinubu), ubangijin da ke sama na kallon ka."
"Har yanzu ba a kammala ba. Yadda ka kula da wahalar da mutane ke ciki shi zai nuna ko gwamnatinka za ta ɗore."

Za ku iya kallon cikakken bidiyon ainhin maganar da Mbaka ya yi a nan

Kotu Ta Soke Zaben Sanatan APC

A wani labarin na daban kuma, kotun sauraron ƙarar zaɓen Sanatan Kogi ta Gaɓas ta yanke hukuncinta.

Kotun ta soke zaɓen Sanatan APC, Jibril Isah inda ta ba hukumar INEC umarnin gudanar da zaɓen cike gurbi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel