Mai Hoto Ya Yanke Kanwar Amarya Daga Hotunan Biki Saboda Ta Ki Ba Shi Shinkafa

Mai Hoto Ya Yanke Kanwar Amarya Daga Hotunan Biki Saboda Ta Ki Ba Shi Shinkafa

  • Wani mai daukar hoto a Najeriya ya fusata bayan an hana shi shinkafa a yayin wani shagalin biki da aka dauke shi aiki
  • Mutumin ya ce an yi hayar shi domin daukar hotunan taron kuma ya kasance a wajen tun a ranar Juma'a don shagalin wankar amarya
  • Mai hoton ya yanke shawarar yin ramuwar gayya kan kanwar amaryar, wacce ke da alhakin rabon abinci

Wani mai dauakr hoto ya bayyana rashin jin dadinsa a wani shagalin bikin aure da ya yi aiki.

A wani labari da ya yadu a soshiyal midiya, mai hoton ya ce kanwar amarya ce ta yi rabon abinci a wajen taron.

Mai hoto ya yanke kanwar amarya daga hotunan biki
An yi amfani da horon don misali ne kawai. Wadanda ke hoton ba su da alaka da batun da ake magana kansa a rahoton. Hoto: Getty Images/Bassey Edoho and Westend61.
Asali: Getty Images

Ya ce lokacin da ya tambayeta abinci, sai matashiyar da ke rike da ragamar rabon abinci ta kunyata shi sosai. A cewarsa, ko ruwa ba a ba shi ya sha ba a bikin.

Kara karanta wannan

Yadda Amarya Ta Fashe Da Kuka a Wajen Biki Bayan Masu Abinci Sun Ki Bayyana, Bidiyon Ya Yadu

Mai hoto ya yanke kanwar amarya daga hotunan biki

Da yake ramuwar gayya kan abun da kanwar amaryar ta yi masa, mutumin ya ce sai da ya tabbatar bata fito a cikin kowani hoto da ya dauka a wajen bikin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi bayanin cewa sai da ya tabbata ta tsaya a gefen kowani hoto ta yadda zai yanketa cikin sauki. Ya kara da cewar:

"Daga baya ta karbi lambata a wajen amaryar tana tambayana dalilin da yasa bata cikin kowani hoto sannan na ce mata ban san cewa tana cikin harkokin bikin ba.

Mutumin mai suna Tobi Oyelami Joel yana martani ne ga wata wallafa da Autograph Foto Studio ya yi. Daga bisani Linda Ikeji Blog ta sake wallafa labarin a Facebook.

Mai hoto da ya yanke kanwar amarya daga hotunan biki ya haddasa cece-kuce

Kara karanta wannan

Baturiya Ta Saki Hotuna Yayin da Ta Fallasa Masoyinta Dan Najeriya Wanda Ya Barta Da Ciki a Turai Don Auren Yar Najeriya

Damilola Oluwatoyin Emmanuel ta ce:

"Wannan ne ramuwar gayya mafi dacewa da na taba gani, ina son gayen."

Chinenye Okochua ta ce:

"Ya yi kyau. Wasu lokutan muma mu zama masu ramuwar gayya. Idan dai har ba zai kawo radadi ga wani ba."

Moshood Abdulrasaq ya yi martani:

"Ramuwar gayya da ta dace, ina alfahari da kai kwamrad."

Wisdom Sampson ya ce:

"Sai ta jira wani bikin."

Wani mutum ya ba ango da amarya gudunmawar galan babu komai

A wani labarin, mun ji cewa wani dan gayya a wajen biki ya gabatar da gudunmawar da ba a saba gani ba, kuma bidiyon ya yadu a TikTok.

A cikin wani dan gajeren bidiyo, mutumin ya tunkari amarya da ango dauke da wani galan mai kalar ruwan dorawa babu komai a cikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng