Labarin saurayin da ya siya gida da mota da kasuwancin kwakwa

Labarin saurayin da ya siya gida da mota da kasuwancin kwakwa

- Wani matashi mai suna Ebenezer ya kasance dan kasuwa ne da ke siyar da kwakwa a babbar kasuwar Saint Johns a birnin Accra

- Ebenezer ya bayyana cewa yana samun a kalla N33,565 a ranar da bai yi ciniki ba

- Matashin dan kasuwar ya kara da cewa, ya mallaki mota da kuma gidan duk da ribar wannan kasuwancin

Wani matashi mai suna Ebenezer, wanda ke siyar da kwakwa a babbar kasuwar Saint Johns kusa sa Achimota a Accra, ya bayyana sirrin kasuwancinsa.

Ebenezer ya bayyana cewa, ya kammala sakandire amma saboda rashin kudi da suka tsinci kansu yasa ya koma siyar da kwakwa.

Matashin dan kasuwar mai suna Ebenezer, ya bayyana cewa ya mallaki gida da mota daga ribar kasuwancinsa na siyar da kwakwa.

Labarin saurayin da ya siya gida da mota da kasuwancin kwakwa
Labarin saurayin da ya siya gida da mota da kasuwancin kwakwa Hoto: Kingsmotion TV
Source: UGC

A yayin zantawa da gidan talabijin na Kingsmotion, ya ce yana samu a kalla N33,565 a rana.

Duk da wasu mutane suna kallon kasuwancin Ebenezer a karami, ya bayyana cewa yana rufa wa kansa asiri da wannan kasuwancin.

Ebenezer ya ce ya siya mota daga kudin da yake samu sannan ya mallaki gidan kansa.

Ya jaddada cewa a kowacce kasuwanci da za ta samesa, ba zai barta ba saboda babu wani kasuwanci da zai kawo masa kudi kamar shi.

Labarin Ebenezer babban darasi ne ga matasa da ke kallon kansu a sun fi karfin wasu nau'ika na kasuwanci.

Kalli bidiyon a kasa:

A wani labari na daban, jami’an ’yan sandan jihar Legas sun kubutar da wani mutum mai suna Abiodun Adeyinka, da yayi yunkurin jefa kansa cikin wani kudiddinfi sakamakon bashin N5m da yayi masa katutu.

Jami’in hulda da al’umma na hukumar ’yan sandan jihar, Bala Elkana, shi ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai.

Ya ba da rahoton cewa “Jami’an ’yan sanda dake sintiri a kan gadar Third Mainland kan titin Abaraje na yankin Ikotun, sun ceto wani bawan Allah da yake yunkurin jefa kansa cikin halaka”.

Inda ya kara da cewa “lamarin ya auku ne ranar juma’a 31 ga watan yulin 2020 da misalin 1:50 na rana, inda daga bisani jami’an suka rankaya da shi zuwa ofishin ’yan sanda dake Bariga domin gabatar da bincike akansa”.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel