Tsabagen Kiyayya Ya Jawo Mawaki Ya na Kiran Sojoji Su yi wa Tinubu Juyin Mulki

Tsabagen Kiyayya Ya Jawo Mawaki Ya na Kiran Sojoji Su yi wa Tinubu Juyin Mulki

  • Charles Oputa bai ki ya ga sojoji sun karbi mulkin Najeriya ba, hakan zai sa ayi waje da Bola Tinubu
  • Tauraron ya nuna kyau kasar nan ta yi koyi da Gabon da Nijar inda sojoji sun hambarar da farar hula
  • Wasu kasashe da ke nahiyar Afrika sun bi tafarkin da Burkina Faso da Gabon su ke na yin juyin mulki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Charles Oputa wanda aka fi sani da Charly Boy wajen waka ya fito ya na jurwayen nuna goyon bayansa ga mulkin sojoji a Najeriya.

A yayin da yake tofa albarkacin bakinsa a dandalin X wanda aka fi sani da Twitter, Charles Oputa ya nuna zai so a hambarar da mulkin farar hula.

Charly Boy ya na cikin gawurtattun magoya bayan Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya zo na uku bayan APC da PDP.

Kara karanta wannan

Ya za a yi? Davido ya ce kudi ne matsalar Najeriya, ya ba da shawarin mafita

Sojojin Mali
Sojojin Mali da su ka yi juyin mulki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shaguben Charly Boy a X

Bai ambaci juyin mulki ba, amma tauraron ya yi sha’awar ganin irin abin da ya faru a wasu kasashen Afrika inda aka kifar da gwamnatoci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Premium Times ta ce mawakin ya ce su na ta addu’o’i, sai ga shi abin ya na tabbata a kasashen nahiyar Afrika da ke makwabtaka da Najeriya.

"Ya Ubangiji mu na addu’a a Najeriya, amma Ka na amsa addu’o’i a Gabon, Nijar, Burkina Faso da Mali.”

- Charles Oputa

Charles Oputa bai yi wani karin haske ba, amma sanannen abu ne cewa ya na da bakar adawa ga Bola Ahmed Tinubu wanda ya ke kan mulki.

Adawar 'Yan Obidient ga Tinubu

Magoya bayan Atiku Abubakar da Peter Obi su na zargin an yi magudi ne a zaben 2023, hakan ya ba jam’iyyar APC damar cigaba da shugabanci.

Kara karanta wannan

"Juyin Mulkin Gabon Ya Faranta Min Rai Sosai", Fayose Ya Bayyana Dalili

Ra’ayin mutane ya fara canzawa da ECOWAS a karkashin jagorancin Bola Tinubu ta yi barazanar yakar kasar Nijar saboda an kifar da farar hula.

A lokacin da ake faman kashe wutan Nijar sai sojojin Gabon su ka hambarar da Ali Bago yadda aka yi tun ba yau ba a Burkina Faso da kuma Mali.

Charley Boy zai yi wa Obi tsirara

Ku na da labari cewa a shekara 73 a Duniya, Charley Boy ya ce zai fito zigidir a Legas muddin Peter Obi ya kai labari a kotun zaben shugaban kasa.

‘Dan takaran shugaban kasa na LP kuma jagoran ‘Yan Obidient yana karar zaben 2023 a gaban kotu, ya na so a rusa nasarar Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel