Wasu Manoma Sun Koka Kan Yadda Ake Sace Musu Amfanin Gona A Jihar Gombe

Wasu Manoma Sun Koka Kan Yadda Ake Sace Musu Amfanin Gona A Jihar Gombe

  • Manoma da dama yanzu su na cikin barazanar asarar amfanin gonakinsu saboda sata
  • Wannan na zuwa ne bayan halin kunci da mutae ke ciki wanda ya haddasa sace-sacen amfani
  • Wasu manoma a jihar Gombe sun bayyana wa Legit.ng Hausa irin matakan da su ke dauka wurin kare amfaninsu

Jihar Gombe - Yayin da ake cikin halin kunci na rayuwa da satar amfanin gona, wasu manoma na daukar mataki don kare amfaninsu.

Wasu manoman na biyan makudan kudade don kula da amfanin gonarsu yayin da wasu ke kwana a gonakin don tabbatar da tsaro.

Manoma a jihar Gombe sun koka kan satar amfanin gona
Wasu Manoma A Najeriya. Hoto: The Guardian.
Asali: UGC

Meye manoman ke cewa a Gombe?

Wasu manoman na biyan masu gadi kudin da ya kai dubu 30 zuwa 50 a wata don tabbatar da tsaron amfaninsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Samu Miliyan 36 Saboda Amfani da Twitter Na Wata 1, Ya Saki Hoton Shaida

A wasu kananan hukumomi da su ka hada da Yamaltu Deba da Kwami da kuma Akko, manoman sun bayyana yadda su ke kula da gonakin na tsawon sa’o’i 24.

Kabir Muhammad, da ke yankin Deba ya ce saboda yanayin satar da ake a gonaki kusan komawa ya yi gonar don kulawa da amfaninsa.

Ya ce:

“Saboda kudaden da na kashe, dole na tsare amfanin gona ta kada asarar ta yi mini yawa ganin halin da mutane ke ciki a yanzu.”

Yayin da wani wanda bai bayyana sunan shi ba ya ce a cikin watanni biyu ya kashe ya kai dubu dari saboda masu gadi a gona.

Ya ce:

“Ina bai wa ‘yan banga dubu 25 ko wace wata su biyu domin kulamin da gona ta kuma haka zanci gaba da har karshe.”

Wasu matakai manoman ke dauka a Gombe?

Wani manomi daga yankin karamar hukumar Kwami, Manu Abdulkadir ya ce suna cikin matsala saboda yawan sata da ake a gonaki inda ya ce a yanzu komai sata ake a gonaki.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki 'Rukunin Gidajen El-Rufai', Sun Sace Wani Mutum

Ya ce bayan satar amfani ga kuma matsalar makiyaya da su ke shiga konaki yayin kiwo wanda hakan na jawo musu asara.

A bangarenshi, Alhaji Muhammadu Malam wanda ke noma a yankin karamar hukumar Akko ya ce a bana abin yafi muni ganin yadda mutane ke cikin mawuyacin hali.

Ya ce kuma duk tausayinka dole ka dauki matakai saboda kai za ka ta shi a tutar babu a karshe.

Ya ce:

“Kusan tattarawa na yi na koma gona saboda a yanzu ne amfanin gona ke nuna kuma dai-dai lokacin da ake cikin wani hali.”

Ya kara da cewa yasan wasu a yankuna da dama da ke biyan ‘yan banga ko masu gadi don kula musu da amfanin gona.

Rikicin Makiyaya Da Manoma Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum 8 A Borno

A wani labarin, Yayin ake rikici kullum tsakanin manoma da makiyaya, rahotanni sun tabbatar cewa an yi asarar rayukan mutane takwas a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Ma’aurata 7 Sun Hada Bikinsu Don Ragewa Juna Zafin Kashe Kudi, Hotunan Sun Yadu

Kwamishinan 'yan sanda a jihar, Abdu Umar shi ya bayyana haka inda ya ce akalla mutane takwas sun rasa rayukansu da kuma kona gidaje 47.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.