Shiru kake ji: Bankin manoma ya koka a kan biliyan N60bn da manoman Najeriya suka ranta

Shiru kake ji: Bankin manoma ya koka a kan biliyan N60bn da manoman Najeriya suka ranta

A yau, Laraba, bankin manoma (BoA) ya bayyana cewar ya fara bin hanyoyin dawo da kudi, fiye da biliyan N60bn, da manoman Najeriya suka karba rance.

Manajan darektan bankin, Mohammed Kabir, ne ya bayyana haka a wurin taro da bankin manoma, reshen Agege, ya shirya a garin Legas.

Mista Kabir, da shugaban bankin shiyyar kudu maso yamma, Idiat Folorunsho, ya wakilta ya ce, bankin zai karbo kudadensa daga hannun manoman domin rabawa ga matasa dake sha'awar yin noma a matsayin sana'a.

Shiru kake ji: Bankin manoma ya koka a kan biliyan N60bn da manoman Najeriya suka ranta
Bankin manoma ya koka a kan biliyan N60bn da manoman Najeriya suka ranta

"Yanzu muna aikin karbo kudi daga hannun manoman da suka karbi rance, kudin sun fi biliyan N60bn."

"Idan manomi ya ranci kudi kuma ya ki dawo da su, ta ya ya kenan bankin zai samu kudin da zai rantawa karin wasu mutanen dake bukatar rance domin bunkasa tasu harkar noman har ta kai ga an samu habakar tattalin arziki?, A cewar mista Kabir.

DUBA WANNAN: Mata sun yi zanga-zanga bayan sakin wanda ya yiwa matar aure fyade

Sannan ya kara da cewar, bankin zai kara bude rassa a sassan kasar nan domin bawa jama'a damar cin moriyar tsarukan bankin.

Mista Kabir ya kara da cewar, wasu manoman har canja adireshi suke yi domin kada su dawo da kudin da suka ranta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng