Gwamnatin Buhari za ta taimakawa Manoma fiye da miliyan biyu da tallafin Naira Biliyan 12.3

Gwamnatin Buhari za ta taimakawa Manoma fiye da miliyan biyu da tallafin Naira Biliyan 12.3

  • Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa manoma miliyan biyu a daminar shekarar nan
  • Andrew Kwasari ya ce za su fara ne da ba manoma miliyan 1.2 tallafin Biliyan 6.15
  • Daga baya ana sa ran wasu manoman fiye da miliyan daya za su ci moriyar tallafin

Jaridar Punch ta ce sama da manoma miliyan 2.2 gwamnatin tarayya ta ke shirin raba wa kudi domin su bunkasa harkar gonarsu a wannan shekarar.

Manoma za su yi murmushi da tallafin Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya za ta raba kudin da ya kai Naira biliyan 12.3 a matsayin tallafi kwanan nan.

Jami’an fadar shugaban kasa sun fada wa jaridar cewa shugaba Muhammadu Buhari ya amince a fitar da tallafin Naira biliyan 6.15 da za a ba manoma.

KU KARANTA: Gwamnan Borno, Zulum ya dauki Manoma fiye da 6, 000 aiki

Manoma miliyan 1.2 za su amfana da sahun farko na wannan tallafin da gwamnati za ta bada.

Kara karanta wannan

Bishop ya bayyana yadda ubangiji ya sanar dashi illolin mulkin shugaba Buhari tun 2015

Andrew Kwasari ya yi magana

Babban mai ba shugaban kasa shawara a kan abin da ya shafi noma, Andrew Kwasari ya bayyana cewa an tantance manoman da za a ba wadannan tallafin.

Kwasari ya ce shugaban kasa ya amince da fitar kudin, sannan NIPSS ya tabbatar da lambobin BVN na asusun banki na wadanda za su amfana da tallafin.

“Manoma miliyan 1.2 za su fara jin shigowar kudinsu a banki ba da dade wa ba. Wasu karin manoma miliyan 1.1 za su samu karin Naira biliyan 6.15.”
Gwamnatin Buhari za ta taimakawa Manoma fiye da miliyan biyu da tallafin Naira Biliyan 12.3
Wasu manoma a Najeriya Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga Malaman Jami’a su koma gona

“Mu na da karin wasu (manoma) fiye da miliyan 1.1, kuma NIPPS ta tabbatar da bayanansu, kuma za a aika sunayen na su ga shugaban kasa domin ya amince.”
“Mun tattara sunayen manoma fiye da miliyan shida a ofishina, za mu bada umarni a fara biyan wadannan manoman da mu ka yi wa rajista tallafin kudi.”

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Hadimin shugaban Najeriyar ya yi kira ga duk wadanda za a ba tallafin, su yi abin da ya kamata wajen bunkasa nomansu, yace za a sa ido a ga abin da suke yi.

Rahotanni sun zo cewa jami'an sojojin ruwa da ke aiki a Legas sun tare buhunan shinkafa 162 da aka yi kokarin a shigo da su Najeriya ta teku daga kasar Benin.

Gwamnati da hukumomin Najeriya suna sa kafar wando daya da masu shigo da shinkafa. An dauki wannan matakin ne domin a karfafa wa manoman gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng