Hukumar EFCC Na Binciken Aikin Wutar Lantarki Ta Mambilla, Inji Ministan Makamashi

Hukumar EFCC Na Binciken Aikin Wutar Lantarki Ta Mambilla, Inji Ministan Makamashi

  • Hukumar EFCC ta fara bincike kan matsaya ta aikin wutar Mambila da gwamnatin Najeriya ke yi tun shekaru da suka gabata
  • Majalisar dattawa ta fara nuna damuwa kan yadda ake aiwatar da aikin wutar Mambila, ta gayyaci masu ruwa da tsaki
  • 'Yan Najeriya sun nuna damuwa tun bayan samun rahoton da ke nuna yaudara ce zalla aikin nan na wutar Mambila

FCT, Abuja - Kwamitin majalisar dattawa ta Najeriya kan wutar lantarki ya bayyana aikin samar da makamashi na Mambilla a matsayin yaudara, duk kuwa da tanadin kasafin kudi na shekara-shekara da gwamnati ke zubawa kullum.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar EFCC ke kan bincikenta na yadda ake gudanar da aikin, in ji ministan makamashi Engr. Abubakar D. Aliyu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Izalah ta yi kididdigan Masallatai da Makarantun ta, tace tanada 112,000

EFCC ta fara bincike kan yadda ake gudanar aikin wutar Mambila
Hukumar EFCC Na Binciken Aikin Wutar Lantarki Ta Mambilla, Inji Ministan Makamashi | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya aikin wutar Mambila yake?

Aikin makamashin Mambila dai sananne ne a gwamnatin Buhari, kuma an nufi samar da wutar lantarki da ta kai megawatts 3,050 idan aka kammala, wanda a yanzu ake kyautata zaton ana ci gaba da aikin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan aka kammala shi, ana sa ran ya zama hanyar samar da wutar lantarki mafi girma a Najeriya, kuma daya daga cikin manyan tashoshin wuta a Afrika.

Nawa gwamnatin Buhari ta kashe kan wannan babban aikin?

Gwamnatin tarayya ta ware N2bn na aikin na Mambila a kasafin kudin 2020. Haka nan, aikin ya samu kason N435m a 2021, N650m a 2022 da kuma N1.1bn a 2023.

Shugaban kwamitin wuta a majalisar dattawa, Sanata Gabriel Suswan (PDP, Benue) ya ce abin takaici ne ace babu abin da za a iya nunawa na aikin duk da kudin da aka kashe.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya yi nadi mai muhimmanci, ya ba wani dan Katsina mukamin babban sakatare

Suswan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ma'aikatar makamashi ke kare kasafin kudin 2023 a gaban kwamishin, rahoton Vanguard ta tattaro.

Kullum abu daya, EFCC ta fara bincike

Sanatan ya kuma bayyana cewa, tun 2017, ana ware kudi na aikin makashin Mambila, amma ba a yi komai ba duk kuwa da irin matsin lamba da majalisa da 'yan Najeriya ke yi a kullum.

A bangare guda, kwamitin ya gayyaci sakataren dindindin na ma'aikatar da sauran masu ruwa da tsaki da su bayyana a gabanta a mako mai zuwa don ba da bahasin abin da ke faruwa da aikin na Mambila.

A nasa jawabin, ministan ya shaidawa kwamitin cewa, tuni hukumar EFCC na bincike kan lamarin, kuma ba za a samu bahasi nan kuda.

Ana ta cece-kuce kan wutar Mambila, gwamnati ta fitar hotunan wutar Zungeru

A wani labarin, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fitar da wasu hotuna a wani bangare na nuna wa 'yan Najeriya tana aikin tashar wutan lanatarki ta Zungeru dake jihar Neja.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Dan Takarar Jam'iyyar Kwankwaso da Tsabar Kudi N326m da Daloli $610,500

A baya, gwamnatin Najeriya ta fara aikin tashar ne tun a shekarar 2013, inda ta nufi kammala aikin a shekarar 2018 wanda kuma hakan bai samu ba, wannan yasa a ka sake sanya watan Disambar 2021 a matsayin lokacin da za a kammala aikin, kamar yadda Wikipedia ta tattaro.

Legit.ng Hausa kafar yanar gizo ta Afrik 21 ta ce an ware makudan kudaden da suka kai dalolin Amurka biliyan 1.3 don wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel